Ebonyi: Jam'iyyar PDP Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamna

Ebonyi: Jam'iyyar PDP Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamna

  • Jam'iyyar PDP ta kudiri aniyar ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun zaɓe na tabbatar da nasarar gwamnan jihar Ebonyi
  • A cewarsa PDP, ba ta gamsu da hukuncin ba musamman kan batun sauya sheƙa da zama mamban jam'iyyar APC
  • Kotun sauraron ƙarar zaben gwamna ta tabbatar da nasarar gwamna Francis Nwifuru na APC a zaɓen 18 ga watan Maris

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ebonyi - Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ebonyi ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin tabbatar da nasarar Francis Nwifuru a matsayin gwamnan jihar.

Jam’iyyar ta kuma bukaci magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu, tare da ba su da tabbacin cewa jam’iyyar PDP za ta ƙwato haƙƙinta a kotun daukaka kara, Punch ta rahoto.

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru.
Ebonyi: Jam'iyyar PDP Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamna Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban PDP na Ebonyi, Ifeanyi Nworie, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan Kotu ta sanar da hukuncin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Ƙazamin Hari Jihar Kaduna, Sun Halaka Mutane da Yawa

A jawabinsa, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba mu gamsu da hukuncin ba. PDP ta amince za ta daukaka kara. Mun gode wa Allah kotun zaɓe ta amince muna da ikon kai batun zama mamba da sauya sheka gaban kotun daukaka kara."
"Muna kira ga mambobinmu baki ɗaya su kwantar da hankalinsu. Jinkirin adalci ba yana nufin ba za a samu adalci bane."

Ɗan takarar APC ya bi sahun jam'iyyarsa

Lauyan ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Ifeanyi Idoko, ya tabbatar da cewa wanda yake karewa zai ɗaukaka ƙara zuwa gaba, Sunnews ta rahoto.

Ya ce ba su ji dadin hukuncin da kotun ta yanke ba kan batun kasancewar Francis Nwifuru mambam jam’iyyar APC.

Idoko ya ce:

“Wannan shi ne mataki na farko, har yanzu muna da kotun daukaka kara. Za mu ƙalubalanci wannan hukunci a kotun daukaka kara. Ba mu gamsu da hukuncin ba."

Kara karanta wannan

Shugabar Karamar Hukumar da Ya Zargi Gwamnan APC da Wawure Kuɗi Ya Shiga Sabuwar Matsala

"Ba mu ji daɗi ba musamman game da batun zamansa mamban APC. Mun kawo koken mu ne bisa sashe na 177 na kundin tsarin mulki. Batun cancanta abu ne da ya shafi gabanin zabe da kuma bayan zabe."

INEC Ta Nuna Damuwa Kan Yanayin Tsaro a Jihohin Kogi da Imo Gabanin Zaben Gwamna

A wani rahoton na daban INEC ta bayyana damuwa kan halin rashin tsaro a jihohin Kogi da Imo yayin da take shirin gudanar da zaben gwamna.

Kwamishinan INEC na kasa, Mallam Mohammed Kudu Haruna, ya bukaci a kara inganta harkokin tsaro domin zaben ya tafi cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262