Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Na Legas Tana Yanke Hukunci: Kai Tsaye

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Na Legas Tana Yanke Hukunci: Kai Tsaye

Legas - Yau, Litinin, 25 ga watan Satumba ne Kotun Sauraron Kararrakin Zabe na jihar Legas za ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar PDP da Labour suka shigar.

Dan takarar gwamna na jam'iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour, da takwararsa na jam'iyyar PDP, Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, suka kallubalantar nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun Legas
Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Na Legas Tana Yanke Hukunci
Asali: Twitter

Ku kasance tare da Legit Hausa a yayin da muke kawo muku yadda ake yanke hukuncin.

Zaben gwamnan jihar Legas na 2023: Takaitaccen bayanin sakamakon zaben

Gabanin fara shari'ar, ga takaitaccen bayanin sakamakon zaben gwamnan jihar Legas na 2023 kamar yadda INEC ta sanar.

Babajide Sanwo-Olu (APC) - kuri'u 762,134

Gbadebo Rhodes-Vivour (LP) - kuri'u 312,329

Olajide Adediran, da aka fi sani da Jandor (PDP) - kuri'u 62,449

Jimillan kuri'u da aka tantance - 1,182,620

Jimillan halastattun kuri'u - 1,155,678

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164