Zaman Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kano Kai Tsaye Daga Kotu

Zaman Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kano Kai Tsaye Daga Kotu

A yau Laraba, 20 ga watan Satumba, 2023, Kotun sauraron ƙararrakin zabe zata yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano.

Jam'iyyar APC da ɗan takararta na gwamna, Nasir Yusuf Gawuna, ne suka shigar da ƙara a gaban Kotun suna kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

Rahoton Aminiya ya nuna cewa Gawuna, wanda ya zo na biyu a sakamakon zaben, da APC suna zargin cewa takarar Abba Gida-Gida ba ta halasta ba saboda bai zama mamban NNPP ba lokacin da aka tsayar da shi takara.

Masu ƙara suna kuma zargin cewa an yi maguɗi a rumfuna da yawa wanda jumullar kuri'unsu ya kai 130,000 kuma idan aka cire waɗan nan kuri'a a kuri'un NNPP, Gawuna ne ya ci zaɓe.

Bayan kammala sauraron kowane ɓangare, Kotun ta zaɓi 20 ga watan Satumba, 2023 domin yanke hukunci.

Legit Hausa ta shirya tsaf domin kawo muku yadda zaman yanke hukunci a Kotun ke gudana kai tsaye, ku biyo mu.

Kotu ta ce Gawuna ne ya ci zaben Kano

Kotun sauraron ƙora-korafen zaɓen gwamnan jihar Kano ta tsige Abba Kabir Yusuf daga matsayin gwamnan, ta ce jam'iyyar APC ce ta lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Ta umarci INEC ta janye takardar shaidar cin zaben da ta bai wa Abba Gida-Gida, ta bai wa Nasir Gawuna, ɗan takarar APC a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓe.

Kotun ta zabtare kuri’u 165,663 daga cikin kuri'un Abba Gida-Gida Yusuf, inda ta ce takardun zaben (165,663) ba su da sutanfi ko sanya hannu, don haka ta ayyana su a matsayin haramtattu.

Magoya bayan APC sun fara murna

Wasu matasa magoya bayan jam'iyyar APC sun fara murna a kan tituna, kan tunanin cewa ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna zai yi nasara a kotun.

Kotu Ta Tafi Hutun Rabin Lokaci

Alƙalan Kotun zaben Kano sun sanar da tafiya hutun rabin Lokaci kuma ana sa da zaran an dawo daga wannan hutu, za su yanke hukunci kan muhimman batutuwaa shari'ar.

Wannan yanke hukunci dai ya ja hankalin 'yan Najeriya musamman ganin yadda Alƙalai suka ƙi halartar Kotu, suka riƙa karanto hukunci ta Intanet yayin da wakiali ke kallo ta majigi.

Daga fara zaman zuwa yanzu, Kotu ta kori karar APC da Gawuna kan halascin takararsa, ta ce masu ƙara ba su hurumin tsoma baki a harkokin NNPP.

Kotu ta yi fatali da korafin INEC da NNPP da kuma Abba Gida Gida na korar karar APC

Kotun sauraran kararrakin zabe ta yi watsi da rokon Hukumar Zabe ta INEC da jam'iyyar NNPP da Abba na korar karar APC inda kotun ta ce za ta binciki hujjojin bangarorin.

Kotu Ta Yi Fatali da Koken INEC

Kotun zaben gwamnan Kano ta yi fatali da ƙorafin jami'in hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC kan cewa lafazin da aka yi amfani da shi a ƙarar ya saɓa wa dokar zabe.

Alkalan Kotun da kuma jam'iyar APC mai shigar da ƙara sun aminta cewa hakan bai saɓa wa kowace dokar zaɓe ba a Najeriya.

Ƙotu Ta Kori Karar APC Kan Halascin Takarar Abba

Kotu ta kori ƙarar jam'iyyar APC da Gawuna kan halascin takarar gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

A cewar Kotun, jam'iyyar APC ba ta da hurumin tuhumar Abba Gida-Gida kan batun da shafi harkokin jam'iyyarsa NNPP.

Magoya Bayan Nasiru Gawuna Sun Yi Sansani a Rushasshen Otal Din Daula Suna Jiran Hukuncin Kotun Zabe

Wasu magoya bayan Nasiru Gawuna, dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Kano, sun yi sansani a wajen otal din Daula wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Usaini Muhammed Gumel, ya ce kotun zaben gwamnan Kano bai wa wadanda aka tantance ne kawai damar shiga harabar kotun.

Alkalai sun fara karanto hukuncin zaben Kano ta manhajar Zoom

Rahotanni sun bayyana cewa Alkalan Kotun zabe sun fara karanto hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano na ranar 18 ga watan Maris, 2023 ta manhajar 'Zoom'

Hakan na tabbatar da cewa Alkalan da ke jagorantar shari'ar ba su halartar Kotun ba a tau amma lauyoyi da wakilan kowane ɓangare na zaune suna kallo da sauraro ta majigi.

Har yanzu ba a bayyana ainihin abinda ya hana alkalai zuwa Kotun ba, amma ama ganin ba zai rasa nasaba da yadda siyasa ta yi zafi tsakanin magoya bayan APC da NNPP ba.

Alamu ya nuna cewa ta intanet za a yanke hukunci a kotu

Jamia'n tsaro sun ce ba su san inda alkalan kotun shari'ar zaben gwamnan Kano suka shige ba, kuma da alama ta intanet za a yanke hukunci.

Wasu manyan jami'an tsaro sun ce dalilin rashin ganin alkalan kotun zaben a kotun na da alaka da yiwuwar yanke hukunci shari'ar ta intanet ta manhajar Zoom.

'Yan siyasa sun yi cirko-cirko a bakin kotu bayan kayyade masu shiga

Hayaniya ta kaure a kotun sauraron kararrakin zabe bayan hana 'yan jarida shiga da waya ko kyamara cikin kotun. Haka kuma 'yan siyasa sun yi tirjiya bayan sanar da su cewa iya mutum 10 ne har da lauyoyinsu aka amince su shiga cikin kotun sauraran kararrakin zaben a Kano.

Shari'ar gwamnan Kano: Shehu Sani ya saki sako mai boyayyen ma'ana

A bangare guda, a yayin da muke sauraron fara shari'ar gwamnan Kano, Sanata Shehu Sani, jigon PDP ya saki sako mai boyayyen ma'ana kan abin da zai faru a shari'ar.

"Liverpool ce za ta yi nasara kan Chelsea a hukuncin wasar kwallon gobe," Sani ya wallafa a shafin X (wanda a baya aka sani da Twitter) a ranar Talata, 19 ga watan Satumba.

Yan sanda sun far wa 'yan jarida a Ƙotu

Jami'an hukumar 'yan sanda sun far wa wasu 'yan jarida suka halarci Kotu zaɓe mai zama a Kano domin ɗauko rahoton yadda zaman yanke hukunci ke gudana.

Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin ‘yan jaridar da lamarin ya shafa akwai Salim Umar Ibrahim na Aminiya da wakilin BBC Hausa, Zahraddeen Lawal.

'Yan sandan da ke bakin aikin sun umarci baki ɗaya 'yan jarida su koma can nesa aƙalla mita 10 daga harabar Kotu, ana haka ne jami'an suka bugi wasu a kai bisa zargin suna ɗaukar hotuna.

Muna fatan Kotu da kori karar - NNPP

Rahoton da wakilinmu ya tattara bayan sanya ranar yanke hukunci, ya nuna cewa Lauyan tawagar lauyiyin NNPP, Barista Bashir T/Wurzici, ya ce suna fatan Kotu ta kori ƙarar.

Muna fatan kotun za ta bi matakin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta bi wajen yanke hukunci saboda al'amuran iri daya ne," in ji shi.

Gawuna zai kwato kujerarsa a Kotu - APC

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton cewa jam'iyyar APC ta ce tana da kwarin guiwar samun nasara a Kotu bisa hujjojin da ta gabatar lokacin shari'a.

Mataimakin APC a Kano, Shehu Maigari, ya ce ba su jin tsoron kamai kuma suna sa ran nasara ga ɗan takarar jam'iyyar Nasir Gawuna.

“Ba mu tsoron komai saboda muna da kwarin gwiwa a kan takardun shaidun da muka gabatar."

An tsaurara matakan tsaro

Bayan sanya ranar yanke hukunci, a jiya Talata aka kara girke ƙarin jami'an tsaro a yankin da Kotun zaɓen ke zama da wasu unguwannin jihar Kano domin tabbatar da zaman lafiya.

Bugu da ƙari, Hukumar Kiyaye Haɗura reshen Jihar Kano (FRSC) ta gargaɗi magoya baya da mazauna su san irin murnar da zasu yi ta hankali bayan sanar da hukunci.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164