Khadija Bukar, Fatima Talba Da Sauran Matan Da Ke Majalisar Dokokin Tarayya Ta 10

Khadija Bukar, Fatima Talba Da Sauran Matan Da Ke Majalisar Dokokin Tarayya Ta 10

Alamu sun nuna ba a cimma fafutukar da ake yi na ganin an samu daidaiton jinsi a majalisar dokokin tarayya ba, bayan rantsar da majalisar dokoki ta 10 a watan Yuni domin su fara ayyukan da aka zabe su a kai.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yayin da kira ga samun karin mata yan majalisa ke kara yawa, adadinsu ya ragu idan aka kwatanta da majalisar dokoki ta tara.

Wasu daga cikin mata yan majalisa
Khadija Bukar, Fatima Talba Da Sauran Matan Da Ke Majalisar Dokokin Tarayya Ta 10 Hoto: Idiat Oluranti Adebule/ Ireti Kingibe/ Dr. Mrs Ipalibo Harry Banigo
Asali: Facebook

Sanatoci mata sun kasance su bakwai a majalisa ta tara inda a yanzu mata 3 ne kacal a majalisa ta 10 yayin da aka samu karuwarsu a majalisar wakilai daga 13 zuwa 16.

Mata yan majalisa a majalisar dattawa ta 10

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ga jerin mata yan majalisa a majalisar dattawa a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Tsohuwar Kwamishiniya Ta Rasu a Jihar Kano

1. Ireti Heebah Kingibe ta Labour Party (LP), tana wakiltan babban birnin tarayya (FCT)

2. Ipalibo Banigo tana wakiltan Ribas ta yamma a jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP).

3. Idiat Oluranti Adebule tana wakiltan Lagas ta yamma a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Mata yan majalisa a majalisar wakilai ta 10

Kamar yadda jaridar Business Day ta rahoto, ga jerin mata yan majalisar wakilai a kasa:

4. Regina Akume (APC) tana wakiltan mazabar Gboko/Tarka a jihar Benue.

5. Maureen Chinwe Gwacham (APGA) tana wakiltan mazabar Oyi/Ayamelum a jihar Anambra.

6. Marie Enenimiete Ebikake (PDP) tana wakiltan mazabar Brass-Nembea jihar Bayelsa

7. Zainab Gimba (APC) tana wakiltan mazabar Bama/Ngala/Kala-Balge a jihar Borno

8. Erhiatake Ibori-Suenu (PDP) tana wakiltan mazabar Ethiope East/Ethiope ta yamma a jihar Delta

9. Mariam Onuoha (APC) tana wakiltan mazabar Isiala Mbano/Okigwe/Onuimo a jihar Imo

10. Kafilat Ogbara Kosofe, (APC) tana wakiltan mazabar Kosefe a jihar Lagos

Kara karanta wannan

Na boye ya fito: Sojoji da DSS sun yi babban aiki, sun gano maboyar tsagerun 'yan tawaye a Najeriya

11. Oriyomi Onanuga (APC) tana wakiltan mazabar Ikenne/Shagamu/Remo North a jihar Ogun

12. Beni Butmak Lar (PDP) tana wakiltan mazabar Langtang North/Langtang ta kudu a jihar Plateau

13. Boma Goodhead (PDP) tana wakiltan mazabar Akuku-Toru/Asari-Toru a jihar Ribas

14. Khadija Bukar Abba-Ibrahim (APC) tana wakiltan mazabar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa a jihar Yobe

15. Fatima Talba (APC) tana wakiltan mazabar Nangere/Potiskum a jihar Yobe

16. Tolulope Akande-Sadipe (APC)tana wakiltan mazabar Oluyole a jihar Oyo

17. Chinwe Clara Nnabuife (YPP) Orumba North/Orumba ta kudu a jihar Anambra

18. Blessing Onuh (APC) Otukpo/Ohimini a jihar Benue state

19. Lilian Obiageli Orogbu (LP) Awka North/Awka ta kudu a jihar Anambra

Tsarin rabawa yan Najeriya N8,000 yaudara ce, Uba Sani

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirin bayar da tallafin kudi na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin yaudara.

Gwamnatin Tinubu ta ba da shawarar rabawa iyalai miliyan 12 N8,000 na tsawon watanni shida don rage masu radadin cire tallafin man fetur da aka yi, shirin da aka jingine daga baya bayan ya sha suka daga yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel