Sanata Omisore Ya Fice Daga Wurin Taron Gaggawa Na APC Bayan Adamu Ya Yi Murabus

Sanata Omisore Ya Fice Daga Wurin Taron Gaggawa Na APC Bayan Adamu Ya Yi Murabus

  • Sanata Iyiola Omisore ya bar babbar sakatariyar APC da ke birnin tarayya Abuja ba tare da ya tsaya ya saurari manema labarai ba
  • Sakataren APC ya bar wurin taron NWC na gaggawa bayan hana shi shiga, a cewarsa ya zo wurin Abdullahi Adamu ne amma bai gansa ba
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan Sanata Abdullahi Adamu ya tura takardar murabus daga shugabancin APC ga shugaba Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya fice daga wurin taron gaggawa na kwamitin gudanarwa (NWC) ba tare da ya saurari 'yan jarida ba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa taron NWC na APC ta ƙasa na gudana yanzu haka a babbar sakatariyar jam'iyya mai mulki da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

Sakataren APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore.
Sanata Omisore Ya Fice Daga Wurin Taron Gaggana Na APC Bayan Adamu Ya Yi Murabus Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sanata Omisore na ɗaya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa NWC da suka isa wurin taron a kan lokaci.

Sai dai jim kaɗan bayan isa wurin, aka ga sakataren APC na ƙasa, Sanata Omisore ya shiga mota ya bar sakatariyar ba tare da ya yi hira da 'yan jarida ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan ne taro na farko tun da aka ji cewa Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga matsayin shugaban APC na ƙasa.

Meyasa aka hana Omisore shiga wurin taron?

Rahoton Vanguard ya nuna cewa kiri-kiri aka hana Sakataren APC shiga ɗaƙin taron NWC, wanda mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ke jagoranta.

Sanata Omisore wanda ya isa Sakatariyar da wuri amma duk da haka ya taras mataimakinsa ya kwace wurin fakin din mota na sakataren APC.

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

Omisore, wanda ya bar Sakatariyar jim kaɗan bayan isarsa, ya ce ya zo ne domin gana wa da Abdullahi Adamu. A cewarsa bai san me ya hana Adamu zuwa sakatariyar ba.

Sakataren tsare-tsaren APC, Nze Chidi Duru, ya ce mambobin NWC na tsammani Omisore zai bi sawun Adamu, ya miƙa takardar murabus daga muƙamin sakatare.

Matawalle Ya Gabatar da Shaidu 19 Domin Kwace Mulki Daga Dauda Lawal a Zamfara

A wani rahoton tsohon gwamna Bello Matawalle ya gabatar da shaidu 19 gaban Kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Zamfara.

Tsohon gwamnan ya ce zaben da aka gudanar cike yake da kura-kurai da maguɗi, bisa haka ya buƙaci Kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262