Abokan Tinubu: Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Gwamnonin Farko Na Dimukradiyya

Abokan Tinubu: Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Gwamnonin Farko Na Dimukradiyya

  • Shugaba Bola Tinubu na daga cikin gwamnonin farko tun bayan dawo wa dimukradiyya a 1999
  • Shugaban ya gana da rukunin gwamnonin shekarar 1999 a ranar Laraba 12 ga watan Yuli a Abuja
  • Tinubu ya musu alkawarin kawo sauyi a kasar da kuma kawo hanyoyin da za su rage radadin cire tallafi

FCT, Abuja - Gwamnonin da aka zaba a shekarar 1999 su ne farkon rukunin gwamnoni a Najeriya tun bayan dawo wa dimukradiyya a kasar bayan mulkin soja.

Mafi yawa daga cikinsu sun rike wasu mukamai bayan kammala wa'adin su a gidajen gwamnatoci daban-daban a jihohinsu, cewar Legit.ng.

Tinubu Da Rukunin Gwamnonin 1999: Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Tsoffin Kurayen
Shugaba Bola Na Daga Cikin Rukunin Tsoffin Gwamnonin Da Suka Yi Mulki Daga 1999 Zuwa 2007. Hoto: @toluogunlesi.
Asali: Twitter

Akwai wadansu abubuwa muhimmai da ya kamata ku sani game da wadannan tsoffin gwamnoni kamar haka:

1. Sakataren Gwamnatin Tarayya

Daya daga cikin tsoffin gwamnonin da suka ziyarci Shugaba Tinubu a ranar Laraba akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, cewar Wikipedia.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gano Hanyar Wargaza LP, Zai Ba Na-Hannun Daman Peter Obi Kujerar Minista

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akume shi ne gwamnan jihar Benue daga shekarar 1999 zuwa 2007 a jam’iyyar PDP kafin daga bisani ya wakilci Benue ta Arewa maso Yamma a majalisar Dattawa a jam’iyyar APC.

2. Tsohon shugaban jam’iyyar APC

Gwamnan jihar Osun, Bisi Akande shi ne farkon shugaban jam’iyyar APC mai mulki.

Akande shi ne gwamnan jihar Osun daga shekarar 1999 zuwa 2003 a jam’iyyar AD wanda Shugaba Tinubu ya ke a lokacin.

3. Tsohon shugaban jam’iyyar PDP

A cikin gwamnonin har ila yau, akwai tsohon shugaban jam’iyyar PDP daga shekarar 2014 zuwa 2015, Ahmad Adamu Mu'azu.

Adamu Mu’azu shi ne gwamnan jihar Bauchi daga 1999 zuwa 2007 kamar sauran tsoffin gwamnonin da suka ziyarci Shugaba Tinubu.

4. Tsoffi da kuma sanatoci masu ci

Daga cikin tsoffin gwamnonin na 1999 wadanda sanatoci ne akwai Orji Uzoh Kalu wanda sanata ne da ya ke wakiltar Abia ta Arewa, sai Adamu Aliero tsohon gwamnan jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Nasara: Gwamnan APC Ya Yi Abu 1, Ya Ceto Mutane 30 Na Jihohin Arewa 3 Daga Hannun 'Yan Bindiga

Orji Uzoh Kalu shi ne gwamnan jihar Abia daga 1999 zuwa 2007 a jam’iyyar PDP mai adawa.

Sai kuma Chimaroke Nnamani na jihar Enugu wanda ya mulki jihar daga 1999 zuwa 2007 kamar sauran gwamnoni.

Ya wakilci Enugu ta Gabas daga 2007 zuwa 2011, sai kuma daga 2019 zuwa 2023 inda ya fadi zabe.

5. Tsohon Minista

Daya daga cikin tsoffin gwamnonin akwai tsohon minister, Niyi Adebayo a ma’aikatar kasuwanci da zuba hannun jari karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Kamar Akande, Adebayo ya mulki jihar Ekiti daga 1999 zuwa 2003 a jam’iyyar AD a wancan lokaci.

"Ban Taba Sanin Zan Zama Haka Ba" Abinda Tinubu Ya Fada Wa Rukunin Gwamnonin 1999

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya fadawa tsoffin gwamnonin da suka yi aiki tare cewa bai taba tsammanin zama shugaban kasa ba.

Tinubu ya fadi haka ne yayin jawabi bayan rukunin tsoffin gwamnonin 1999 sun kai masa ziyara a fadarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni 36 Su Aiko Masa Sunayen Mutanen Da Zai Ba Mukami

Tsoffin gwamnonin sun kai masa ziyara ne don nuna goyon bayansu ga abokin nasu da suke tare tun 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel