Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni 36 Su Aiko Masa Sunayen Mutanen Da Zai Ba Mukami

Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni 36 Su Aiko Masa Sunayen Mutanen Da Zai Ba Mukami

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da kungiyar Gwamnonin Najeriya watau NGF a fadar Aso Rock Villa
  • A wajen taron Shugaban kasa ya fadawa Gwamnoni su ba shi sunayen wadanda suka dace da mukamai
  • Shugaban NGF, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce babu batun jam’iyya wajen rabon kujerun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Gwamnonin jihohi su kawo sunayen mutanen da su ka cancanta a ba mukamai.

Leadership ta fitar da rahoto cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ajiye batun jam’iyya, ya nemi kowane Gwamna ya kawo masa mutane.

Za a duba wadanda su ka dace, a ba su mukamai a majalisun da ke kula da hukumomi, ma’aikatu da kuma cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

NGF ta yabawa Tinubu

Shugaban kungiyar gwamnoni nan NGF, AbdulRahman AbdulRazaq, ya shaida haka a jawabin karshen taron gaggawan da suka yi a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Wasu Darusa 4 Da Aka Fahimta Daga Nasarar Tinubu Da Shettima a Zaben 2023, El-Rufai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da jawabin a yammacin Talata.

Gwamna AbdulRazaq ya ce NGF ta yabi gwamnatin Tinubu game da yadda ta nuna jagoranci, ta ba kowane Gwamna dama duk da sabanin jam’iyya.

An bukaci su kawo mutanen da suka cancanta domin a ba su mukamai a majalisun ma’aikatu.

Za a maye gurbin wadanda aka sauke

Jaridar Sun ta ce hakan yana zuwa ne bayan shugaban kasa ya ruguza kusan duk majalisun ma’aikatun gwamnatin tarayya a ranar 19 ga Yuni.

Daga lokacin aka fahimci gwamnatin Tinubu za ta maye gurbinsu ba tare da bata lokaci ba.

Matsalar ambaliya a Jihohi

A cewar Mai girma Abdulrazak, Gwamnonin jihohi sun dauki matakan gaggawa domin magance ambaliyar ruwa saboda gudun fama da fatarar abinci.

Gwamnonin sun saurari jawabi daga bakin hukumomin NEMA da NiMet, kuma sun shirya hada-kai da gwamnatin tarayya domin ganin an samu mafita.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Wa za a ba Minista a Bauchi?

Kun ji labari cewa mun tambayi wani matashin ‘dan siyasa a Bauchi ko wa ya fi dacewa ya zama Minista daga jihar, sai ya ce mutane uku ne a kan gaba.

Wannnan ‘dan siyasa ya ce duka mutanen da ake magana sun cancanta, sai dai su na neman wanda zai iya farfado da APC kuma ya tafi da kowane bangare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel