Kungiyar Farar Hula Ta Nemi a Binciki Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Kan Yadda Ya Tara Dukiyarsa

Kungiyar Farar Hula Ta Nemi a Binciki Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Kan Yadda Ya Tara Dukiyarsa

  • Wata gamayya ta kungiyoyin farar hula ta bukaci a binciki yadda gwamnan Zamfara ya tara dukiyarsa
  • Kungiyar ta ce ba wai ta na adawa da tara kudi da mutane suke yi ba ne, ta na so ne dai ya kasance an san hakikanin hanyar neman mutum
  • Kungiyar ta ce abin mamaki ne a ce gwamnan na da tarin dukiyar da ta kai $5b ba tare da mallakar wata masana’anta ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legas - Wata gamayyar kungiyoyin farar hula, ta bukaci a gaggauta bincikar gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, don sanin yadda ya mallaki gidajen da ya ce yana da su a kasashen Faransa, Amurka da Ingila.

Shugaban kungiyar, Kwamared Femi Lawson, ne ya bayyana hakan a wani taro na manema labarai a Legas kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Kai Ziyarar Bazata Babban Asibiti, Ya Kama Ma'aikatan Lafiya Dumu-Dumu Su Na Aikta Laifi

An bukaci an binciki yadda Dauda Lawal ya tara kudade
An bukaci an binciki gwamnan Zamfara don ji yadda ya tara dukiyarsa. Hoto: Mugira Yusuf
Asali: Facebook

Kungiyar ta bayyana dalilinta na son a bincikin gwamnan

Lawson ya bayyana cewa kungiyar ba ta na adawa da tara dukiya da mutane suke yi ba ne gabanin neman shugabanci, sai dai ta na son ya zamto cewa hanyar samun kudin mutum a bayyane take.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa yana da kyau Gwamna Dauda Lawal ya bayyanawa duniya yadda ya tara wadannan makudan kudaden nasa.

Sannan ya bayyana cewa yana da kyau gwamnan ya zama shugaba abin koyi ta hanyar bayyanar da duka kadrorinsa da yadda ya tara dukiyarsa gabaan hukumar da’ar ma’aikata.

Kungiyar ta ce ‘yan jihar Zamfara bas a amfani da arzikin da ke jihar

Kungiyar ta ce ta dauki matakin da ta dauka ne saboda yanzu Najeriya na cikin wani mawuyacin hali fiye da kowane lokaci.

Ta ce batun tarin bashi da matsalolin tattalin arziki da ake ciki a yanzu ne ya sa ta ke iya bakin kokarinta wajen ganin an yi abubuwan da suka dace.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah Ta Nemi a Saki Mambobinta Da Aka Tsare a Anambra Ba Tare Da Sun Aikata Laifi Ba

Lawson ya kuma bayyana cewa sun mayar da hankalinsu kan Zamfara kadai ne, saboda la’akari da irin arzikin da ubangiji ya yi wa jihar na Zinare ba tare da suna amfana ba.

Kungiyar ta ce ta na mamakin yadda za a ce gwamnan ya mallaki dukiyar da ta kai dala biliyan biyar ($5b) ba tare da yana da wata babbar masana’anta ba.

Ta ce ko attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, Aliko Dangote, dala biliyan sha biyar ($15b) gare shi duk da irin tarin kadarorinsa.

Kwanaki kadan bayan rantsar da shi, Dauda Lawal a hirarsa da RFI Hausa, ya musanta rade-radin da ake ta yayatawa na cewar ya mallaki naira tiriliyan tara.

Tinubu ya dorawa Yarima alhakin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan aikin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, kuma tsohon sanata, Ahmed Sani Yariman Bakura.

Kara karanta wannan

Ahir dinku: Tinubu ya dagawa Turawa EU yatsa kan rahoton zaben 2023, ya caccake su

Yarima ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya dora alhakin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara a hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel