Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi

Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi

  • Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023
  • Yayin wannan ziyara, gwamnan ya tarad da malaman lafiya suna siyar da maganin da aka tanadar na kyauta ga kananan yara
  • Lamarin dai ya fusata gwamnan kuma ya sha alwashin cewa ba zai bar wannan laifin ya wuce haka nan ba

Jigawa State - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse, babban birnin jiha ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023.

Premium Times ta rahoto cewa yayin wannan ziyara, gwamna Namadi ya kama ma'aikatan lafiya suna siyar da magungunan da ake rabawa kananan yara kyauta.

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa.
Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Ba Zata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi Hoto: Jigawa State New Media Office
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Hamisu Gumel, ya ce mai gidansa ya kira gurbataccen aikin da ya samu ma'aikatan lafiya na yi da cin amana da zagon kasa.

Kara karanta wannan

Aminat Yusuf: Gwamnatin Edo Ta Bayyana Yawan Kudin Da Za Ta Dunga Biyan Dalibar LASU Da Ta Kafa Tarihi

Gwamnan ya ce hakan ya saɓa wa tsarin gwamnatinsa na samar da magunguna ga kananan yaran da ba su cika shekaru 5 ba kyauta da kuma iyaye mata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mai girma gwamna ya yi takaicin gano cewa marasa lafiya musamman kananan yaran da ba su kai shekara 5 ba sai sun sayi magani a Asbitin."
"Wannam ya saɓa wa tsarin gwamnatin jiha na samar da kiwon lafiya kyauta ga yaran da basu wuce shekara 5 a faɗin jihar Jigawa. Kaso 70 na yaran da gwamna ya yi magana da su da mata masu shayarwa sun ce sayen magani su ke."
"Nan take fuskar gwamna ta ɓaci kana ya ce wannan ba ƙaramin cin amana bane kuma duk mai hannu a aikata hakan zai ɗanɗana kuɗarsa," inji Gumel.

Gumel ya ƙara da cewa mai girma gwamna bai ji daɗin yanayin da ya tsinci asibitin ba, wani ɓangaren babu wuta kuma dukka da ma'aikata da masu jinya suna zaune a duhu.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir Ya Bayyana Watan Da Za A Fara Tallafin Karatu Na Dalibai Zuwa Kasashen Waje

Jami'in gwamnatin Jigawa, wanda yana cikin tawagar gwamna ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa lallai gwamna Namadi bai ji daɗin abinda ya gani ba a Asibitin.

Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da yan jarida, ya ce tun asali korafe-korafe sun yi yawa kan lalacewar babban Asibitin shiyasa gwamna ya ɗauki wannan matakin.

Ya ce:

"Ina tabbatar maka zaka ga abinda gwamna zai yi kan wannan abun, ya fusata sosai, magungunan kyauta ana siyarwa, kayan aiki sun lalace duk da kasafin da ake ware wa Asibitin."

Haka nan wata 'yar cin birnin Dutse, Aisha Habib, ya faɗa wa wakilin mu cewa ba karamin daɗi suka ji da wannan ziyara da gwamna ya kai ba.

a cewarta, "Babban Asibiti ne, nan muke zuwa amma idan kaga yadda ya koma ba'a cewa komai, bana tunanin akwai wani ɗan garin nan da bai ji daɗi ba. Muna yi wa gwamnan mu fatan Alheri, Allah ya taimake shi."

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Kotu Ta Soke Korar da Jam'iyyar PDP Ta Yi Wa Tsohon Gwamna, Nnamani

A wani rahoton na daban kuma Kotun tarayya mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta soke korar da aka yi wa tsohon gwamnan Enugu daga PDP.

Yayin da yake yanke hukunci ranar Litinin, mai shari'a James Omotosho, ya yanke cewa ba'a yi wa Sanata Nnamadi adalci ba duba da tanadin kundin tsarin mulkin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel