Sabon Gwamna Ya Kori Hakimai, Masu Unguwanni Ana Shirye-Shiryen Hawan Sallah

Sabon Gwamna Ya Kori Hakimai, Masu Unguwanni Ana Shirye-Shiryen Hawan Sallah

  • Dauda Lawal Dare ya dakatar da wasu Masu unguwanni da Hakimai da Bello Matawalle ya nada
  • Gwamnan Zamfara ya sallami manyan sakatarorin gwamnatin jihar domin gyara aikin gwamnati
  • Sanarwar ta fito daga ofishin Abubakar Nakwada a matsayinsa na Sakataren gwamnatin jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara – Gwamna Dauda Lawal Dare ya tsige manyan sakatarorin gwamnatin jihar Zamfara, sannan ya dakatar da wasu daga cikin shugabannin gargajiya.

A ranar Laraba, Premium Times ta rahoto cewa Mai Girma Dauda Lawal Dare ya tsaida Hakimai da Masu unguwannin Zamfara da Bello Matawalle ya nada.

Gwamnatin Zamfara ta ce wannan ya na cikin gyare-gyaren da ta fito da su domin ayi maganin barnar da Gwamnatin Matawalle ta rika tafkawa a lokacinta.

Gwamnan Zamfara
Gwamna Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

SSG ya zanta da manema labarai

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Nakwada ya shaida haka lokacin da ya kira taron manema labarai a ranar Talata, yana bayanin facakar da aka yi a baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abubakar Nakwada ya zargi gwamnatin APC da ta shude da yin facaka, an kashe N50bn da sunan gyara gidan gwamnati da N10bn domin gina filin jirgin sama.

An sauke duka Hakiman da aka kirkira a Disamban 2022, sannan an ruguza manyan sakatarorin gwamnati da aka nada bayan babban zaben 2023.
"Za a zauna domin fitar da tsarin gyara ma’aikatun gwamnati domin a rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da mulki da kuma inganta kyawun aiki."

- Abubakar Nakwada

Leadership ta ce Dauda ya kama hanyar kawo gyara wajen harkar aikin gwamnati, ya ce nan gaba kadan zai sanar da Zamfarawa matakan da aka dauka.

A cewar Nakwada, jihar Zamfara ta na shirin durkushewa da Matawalle ya bar mulki.

Almubazzaranci da dukiyar talakawa

"Gwamnatin (ta baya) ta rika facaka da almubazzaranci tare da satar kadarorin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Hankalin Shugabannin Ma’aikatu ya Tashi a Sakamakon Zazzagar da Tinubu Yake yi

Abin bakin ciki ne yayin da wasu jihohin su ka samu cigaba, har yanzu mu na fama da tulin matsaloli a sanadiyyar hadama da rashin kishin gwamnatin baya.

- Abubakar Nakwada

Gwamnatin PDP ta zargi Matawalle da kin biya daliban jihar kudin jarrabawar WAEC da NECO, Nakwada ya ce a halin yanzu sun biya wadannan kudi.

Tuki sai da takardar POC

A makon nan ne labari ya fito cewa Gwamnatin tarayya ta wajabtawa duk masu amfani da abubuwan hawa biyan haraji domin su mallaki shaidar POC.

Masu tirela, tifa, gingimari, karamar mota, keke napep, babur duk sai sun biya akalla N1000 a duk shekara. Mun fahimci jama’a sun yi tir da sabon tsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel