Hankalin Shugabannin Ma’aikatu ya Tashi a Sakamakon Zazzagar da Tinubu Yake yi

Hankalin Shugabannin Ma’aikatu ya Tashi a Sakamakon Zazzagar da Tinubu Yake yi

  • Akwai yiwuwar Bola Ahmed Tinubu ya fatattaki Shugabannin ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati
  • Abin da ya jefa jami’o’i cikin dar-dar shi ne sauke Shugabannin majalisun sa ido da aka yi a kwanaki
  • Wasu shugabannin sun yi shekara da shekaru su na rike da kujerar gwamnatin tarayya a Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugabannin wasu daga cikin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya sun shiga dar-dar tun da aka sauke majalisar da ke kula da aikinsu.

Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya tada hankalin shugabannin, ta kai wasu sun koma jiran ranar sallama.

Akwai wasu da su ke ganin sabon shugaban kasar zai bari su karasa wa’adinsu saboda ganin sun yi abin-a-yaba a lokacin Muhammadu Buhari.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a wajen taro Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

An shiga dar-dar a ko ina a gwamnati

Kara karanta wannan

Siyasar Majalisa: Atiku Zai Tsinci Kan Shi a Sabon Rikici da ‘Yan G5 a Kan Tambuwal

Ziyarar da jaridar ta kai zuwa wasu ofisoshin gwamnati da ke Abuja da Legas ya tabbatar da irin halin firgicin da ake ciki tun bayan 19 ga watan Yuni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da wasu shugabannin su ke cikin firgici, da-dama daga cikinsu sun gagara yin aiki domin hankalinsu ya rabu biyu tun da aka canza gwamnati.

Rahoton ya ce an samu shugaban wata ma’aikata da yake neman ranar da za a aiko masa da takardar sallama domin ya yi shekaru takwas a mukaminsa.

Daga cikin shugabannn akwai wadanda su ke da kyakkyawar alaka da Bola Tinubu tun ya na Gwamna, ire-irensu su na sa ran ba za su rasa kujerunsu ba.

Manya sun rude bayan tafiyar Buhari

Hadiman wasu shugabannin hukumomin tarayya sun fadawa jaridar cewa iyayen gidansu sun rude, an rasa gane inda su ka dosa, amma sun gaza yin murabus.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Siyar Da Filin Da Aka Sanya Cikin Wadanda Za a Rusa, Rimingado Ya Magantu

Sannan ba za a rasa wadanda su ke ganin za a iya canza masu hukumomi ko cibiyar aiki ba.

Har a shafin Twitter, Legit.ng Hausa ta lura da yadda wasu ma’aikatan su ke ta addu’ar Shugaba Bola Tinubu ya kori shugabanninsu, ya nada sababbi.

A ranar da aka tsige shugabannin majalisun sa ido a ma’ikatun, wasu su ka rika murna da fatan an kori shugaban kamfaninsu da ke karkashin gwamnati.

Shi kuma wani matashi ya ce hakan bai yi masu dadi domin sun ci burin samun aiki kafin gwamnati ta juya, a cewarsa sun dade su na zaman kashe wando.

A yammacin Litinin aka ji labari Shugaban hukumar NUC na kasa, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya rubuta takardar ajiye aiki, zai koma aikin jami’arsa.

Abubakar Rasheed ya yi shekaru a kujerarsa, kuma ya na da ragowar shekaru a ofis amma ya yi murabus kafin sabuwar Gwamnati ta fara tsige shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel