Buhari: Abin Da Ya Sa Na Bar Tinubu Da Aikin Cire Tallafin Man Fetur Idan Ya Hau Mulki

Buhari: Abin Da Ya Sa Na Bar Tinubu Da Aikin Cire Tallafin Man Fetur Idan Ya Hau Mulki

  • Muhammadu Buhari ya yi maganar hikimar hakura da janye tallafin fetur kafin ya bar Aso Rock
  • Tsohon Shugaban ya ce da gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, APC za ta iya rasa zaben 2023
  • A jawabinsa ta bakin Garba Shehu, Buhari ya yabi yadda Shugaba Bola Tinubu ya fara mulkinsa

Abuja - A ranar Litinin, Muhammadu Buhari ya yi karin haske a kan hikimar hakura da janye tsarin tallafin man fetur kafin ya bar fadar Aso Rock.

Vanguard ta ce Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin Garba Shehu, ya na mai cewa da fetur ya kara tsada, jam’iyyar APC za ta iya fadi zabe.

Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi a matsayin martani ga masu sukar tsohon shugaban saboda ya gagara yin abin da Bola Tinubu ya yi tun wuri.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya Yau, Akwai Yiwuwar a Nada Ministoci Bayan Sallah

Buhari
Bola Tinubu da Muhammad Buhari a Landan Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Bincike da aka yi ya nuna APC ba za ta kai labari a zaben 2023 idan fetur ya tashi ba, saboda tsoron Bola Tinubu ya sha kashi, aka dakatar da shirin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tallafin da Gwamnatin Buhari ta cire

Mai magana da yawun tsohon shugaban Najeriyan ya ce a lokacin da Buhari ya karbi mulki, ana biyan tallafn lantarki, na takin zamani, fetur da kananzir.

Shehu ya ce gwamnatin tarayya ta kan dauki dawainiyar masu zuwa sauke farali a Saudi Arabiya da Jerusalem, kafin Buhari ya bar ofis, sai da ya soke su.

Duk da bai yi waje da tsarin tallafin man fetur ba, gwamnatin mai gidansa ta kawo karshen cushe a kasafin kudi da sauran tallafi masu biliyoyi a shekara.

Muhammadu Buhari ya yabi Tinubu

Bugu da kari, tsohon ‘dan jaridar ya ce gwamnatin Tinubu/Shettima ta fara mulki da kyau, ta na daukar matakan da su ka dace ba tare da an samu rikici ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ya Kamata Tinubu Ya Binciki Buhari, Tsoffin Ministoci, Tsoffin Shugabannin Tsaro Da Sauransu

Shugaba Buhari ya yabi magajinsa watau Bola Tinubu a kan tsare-tsaren tattalin arzikin da ya dauko, Buhari ya nuna ba zai so ya dauke hankalinsa ba.

"Batun janye wani tallafi, a halin da mu ka shiga ciki – da kowane irin hali aka tsinci kai – ba matakin da shugaban Najeriya zai dauka shi kadai ba ne.
Babu shugaban kwarai da zai hura wuta a lokacin da ake gobara. Akwai zabe a gabanmu, maganar gasiya dole Buhari ya yi abin da zai ba APC nasara.

An nada CMD a asibitin OAUTHC

Rahoto ya zo inda aka fahimci cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta na neman kawo karshen rikicin da aka shekara ana yi a asibitin koyon aiki na OAUTHC.

Kwanaki kadan da nada ta, sabuwar Hadimar shugaban kasa, Dr. Salman Ibrahim Anas ta yi maganin rigimar shugabancin, ta nada shugaban rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel