Yadda Na Samu Kudi, Na ba Wike Gudumuwar Takarar N200m – Shugaban Majalisa

Yadda Na Samu Kudi, Na ba Wike Gudumuwar Takarar N200m – Shugaban Majalisa

  • Godswill Akpabio ya yi kokarin wanke kan shi daga zargin taba asusun gwamnati wajen kamfe
  • Nyesom Wike ya ce shugaban majalisar ya ba shi gudumuwar miliyoyi da yake takarar Gwamna
  • Sanata Akpabio yake cewa wadannan kudi sun fito ne daga guminsa ba baitul-malin Akwa Ibom ba

Rivers - Godswill Akpabio ya yi karin haske game da labarin da yake yawo cewa ya ba Nyesom Wike gudumuwar makudan kudi da yake takara.

A lokacin da yake neman zama Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya bada labarin irin gudumuwa mai tsoka da ya samu a hannun Godswill Akpabio.

Shi kuma Akpabio zai sauka daga kujerar Gwamnan jihar Akwa Ibom ya zama Sanata a 2015.

Wike, Akpabio, Sanwo Olu
Taron da aka shiryawa Nyesom Wike Hoto:pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Wike ya samu nasara a zaben a karkashin jam’iyyar PDP, amma daga baya abokin na sa wanda shi ne shugaban majalisar dattawa a yau, ya koma APC.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Arewa Ya Yi Shiga Mai Ban Mamaki, Ya Kai Ziyarar Bazata Wani Asibiti a Keke Napep

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake jawabi a wajen bikin da aka shiryawa tsohon Gwamnan na jihar Ribas, Akpabio ya bayyana silar wadannan kudi domin gujewa zargi.

Kudin ajiya ne ba dukiyar A/Ibom ba

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi, an ji shugaban majalisar ya na cewa halaliyarsa ya ba Wike gudumuwa ba dukiyar baitul-mali ba.

Ganin a lokacin ya na rike da gwamnatin jiha a hannunsa, Akpabio ya ce ya samu kudin ne daga ajiyar da ya yi a lokacin yana kamfanin sadarwa.

Baya ga haka, ‘dan siyasar ya tabbatar da cewa ya biya gwamnatin Legas harajin kudin.

Gaskiya ta fito?

Da bayanin, ana sa ran tsohon Gwamnan ya rufe bakin masu suka cewa an yi amfani da dukiyar al’umma wajen taya PDP yakin neman zabe a Ribas.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Dalilin da Ya Sa Ya Marawa Akpabio Baya Ya Zama Shugaban Majalisa

Wadanda su ka halarci bikin da aka shiryawa Wike a coci sun hada da shugabanin majalisa, jagororin APC da manyan APC irinsu Abdullahi Ganduje.

A jawabinsa, Akpabio bai ambaci kudin da ake magana ba, amma Wike ya ce N200m ne. Vanguard ta fitar da wannan labari a cikin farkon makon nan.

Zaben shugabannin majalisa

Kwanaki aka ji labarin yadda Sanatoci su ka yi samakko wajen zuwa majalisar tarayya a ranar zaben shugabanni, Opeyemi Bamidele ya shaida haka.

Sanatan jihar Ekiti ta tsakiya ya ce sun yi kwanaki babu barci saboda yakin neman zaben Akpabio/Barau, a karshe su ka yi galaba a kan Abdulaziz Yari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel