Abin Da Ya Jawo Mu Ka Hallara Majalisa Tun Karfe 4:00 Na Asuba, In Ji Sanatan APC

Abin Da Ya Jawo Mu Ka Hallara Majalisa Tun Karfe 4:00 Na Asuba, In Ji Sanatan APC

  • Opeyemi Bamidele mai wakiltar Ekiti ta tsakiya ya ce sai da suka yi da gaske a zaben majalisa
  • Sanatan ya rike Mataimakin Darekta Janar na yakin zaben Akpabio/Barau a karkashin APC
  • ‘Dan majalisar ya ce sun kwana babu barci domin ganin Sanata Akpabio ya gaji Ahmad Lawan

Abuja - Sanata mai wakiltar Ekiti a karkashin jam’iyyar APC, Opeyemi Bamidele, ya yi bayanin abin da ya faru a ranar zaben shugaban majalisa.

Daily Trust ta rahoto Opeyemi Bamidele ya na tabbatar da cewa tun karfe 4:00 na asuba su ka iso harabar majalisa domin shirin rantsarwa da za ayi.

Sanata Bamidele wanda shi ne Mataimakin Darekta Janar na yakin neman zaben Akpabio/Barau ya ce sun yi sammako ganin abin da aka yi a 2015.

Sanatan APC a Majalisa
Zaman Majalisar Dattawa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

‘Dan siyasar ya ce rashin sammako ya cuce su wajen zaben shugabanni a majalisa ta takwas.

Kara karanta wannan

G5: Yadda Jagororin PDP Su Ka Yi Watsi da Jam’iyyarsu, Su Ka Bi APC a Zaben Majalisa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meya faru a zaben 2015?

Bukola Saraki ya ki yarda ya sallamawa matsayar APC a wancan lokaci, ya shiga takara duk da shugabannin jam’iyya na tare da Ahmad Lawan.

Rahotanni sun ce Bukola Saraki ya lallaba ya shiga majalisar dattawa ne a lokacin da wasu Sanatocin APC ke kokarin yin wata ganawa a dakin ICC.

A lokacin da ake cewa Muhammadu Buhari zai zauna da zababbun majalisa ‘yan jam’iyyarsa aka yi wuf aka zabi Saraki da kuma Ike Ekweremadu.

A ranar Talata Bamidele ya yi magana wajen rantsar da Godswill Akpabio, Tribube ta rahoto shi ya na cewa sun kwana tsaye saboda ganin an yi nasara.

‘Dan majalisar ya kuma ce Ahmad Lawan ya taka rawar gani har Akpabio mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso yamma ya doke Abdulaziz Yari.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

“Na yi kwanaki biyu ba tare da barci ba duk saboda Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisa.
Mun shigo majalisa da kusan 4:00 na safe domin gujewa abin da ya faru a 2015. Nasarar ba za ta yiwu ba tare da tsohon shugaban majalisar dattawa ba.

- Opeyemi Bamidele

Yari bai ci zabe ba

Rahoto ya zo cewa Godswill Akpabio ya yi galaba a kan Abdulaziz Yari wajen zama sabon shugaban majalisar dattawa kamar dai yadda APC ta ci buri.

Sabon Shugaban Majalisar ya fito daga Kudu maso kudu. Sanata Akpabio ya tserewa tsohon Gwamna Abdulaziz Yari ne da ratar kuri’u 17 rak a takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel