Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Sanadin Rasa Rayyuka 2 Da Lalata Gidaje 20 a Jigawa

Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Sanadin Rasa Rayyuka 2 Da Lalata Gidaje 20 a Jigawa

  • Mutane biyu ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wata mummunar iska mai ƙarfi da aka yi ranar Litinin a wasu sassa na jihar Jigawa
  • Shugaban Ƙaramar Hukumar Ringim, Shehu Sule-udi, ya ce iskar ta kuma bata gidaje guda 20 a ƙauyukan Larabawa da Hambarawa
  • Mutanen da da lamarin ya rutsa da su sun yi kira zuwa ga gwamnati, masu hannu da shuni da sauran ƙungiyoyi da su zo su taimaka musu bisa wannan iftila'in da ya faɗa musu

Jigawa - Shugaban Ƙaramar Hukumar Ringim da ke jihar Jigawa, Shehu Sule-Udi, ya bayyana cewa akalla mutane biyu ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a wata mummunar iska mai ƙarfi da aka yi a yankin, ranar Litinin da ta gabata.

Mista Sule-Udi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ofishinsa ranar Laraba, inda ya ce iskar ta kuma lalata gidaje akalla guda 20.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Je da Kansa, Ya Baiwa Waɗanda Harin Yan Bindiga Ya Shafa Tallafin Kuɗi da Abinci

Iska ta ja rasuwar mutane 2 a Jigawa
Iska mai karfi ta janyo rasa rayukan mutane 2 da lalata gidaje 20 a Jigawa. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Shugaban ya bayyana yadda lamarin iskar ya faru

Ya ce an samu asarar rayukan na mutanen biyun ne a ƙauyukan Larabawa da Hambarawa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce lamarin ya faru ne da tsakiyar dare, wanda kuma ya janyowa mutane da dama rasa muhallansu.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mara dadi, sannan ya yi alƙawarin bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

Mutane sun nemi Gwamnatocin Jigawa su kawo musu ɗauki

Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, a zantawarsu da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), sun yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su tallafa musu.

Aminu Hadi, ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, ta hanyar rasa gidansa da ya yi, ya bayyana lamarin a matsayin abu mai ban tsoro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Hadi ya yi kira ga masu hannu da shuni, ƙungiyoyi da kuma gwamnati da su kawo musu ɗauki bisa iftila'in da ya fada musu, kamar yadda The Eagle Online ta wallafa.

Ya kuma yaba wa ƙaramar hukumar bisa kawo musu ɗauki tare da bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

Sanata mai faɗa aji ya rasa ransa a ƙasar Amurka

A wani labarin da muka wallafa muku a baya, kun ji cewa Sanata Annie Okonkwo, tsohon sanatan da ke wakiltar Anambra Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya, ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Amurka.

Okonkwo ya rasu ne dai bayan fama da ya yi da matsananciyar rashin lafiya.

Wasu daga cikin yan uwansa ne suka shaidawa manema labarai batun rasuwar tasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel