An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni a Game da Talakawa

An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni a Game da Talakawa

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da Gwamnonin Najeriya, ya nuna sai an yi maganin talauci a kasar nan
  • Shugaban kasar yana so a ajiye ra’ayin siyasa a gefe guda, ayi kokarin ragewa talaka radadin talauci
  • Tinubu ya kuma roki kasashen Turai su taimakawa Najeriya ta fuskar tsaro da kuma maganin talauci

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Gwamnoni su hada-kai da gwamnatin tarayya domin ganin yadda za a magance talauci a kasar nan.

Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan kira ne lokacin da ya zauna da kungiyar gwamnonin Najeriya a Aso Rock dazu, Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Sabon shugaban kasar ya nunawa Gwamnonin jihohi ba zai yarda da yanayin talaucin ba.

Bola Tinubu
Tinubu da wasu Gwamnoni Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya fadawa jagororin su ajiye duk wani sabanin siyasa, su hada karfi da karfe domin ganin sun kauda talauci, sun fitar da jama’a daga kunci.

Kara karanta wannan

Naɗin Muƙamai: Kiristocin Najeriya Sun Fadawa Tinubu Abin da Suke So a Mulkinsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mu na ganin tasirin talauci ga jama’armu. Talauci ba gado ba ne, daga al’ummarmu ne. Matsayarmu ita ce dole mu yaki talauci.

A ajiye bambancin siyasa, mun zo nan ne saboda Najeriya da kuma yadda za a gina jama’a.

Mu ‘yan dangi daya ne da ke gida guda, mu na barci a dakuna dabam. Idan mu ka dauki abubuwa a haka, za mu fito da jama’a daga talauci.

Jaridar ta ce jawabin shugaban kasar ya fito ne ta bakin Darektan yada labarai, Abiodun Oladunjoye.

Dakunan da shugaban kasar yake magana su ne jam’iyyun siyasa, amma gidan shi ne Najeriya, ya ce bai dace ayi wasa da kuma hadin-kan al’umma ba.

Tinubu ya yi waya da EU

The Cable ta ce Oladunjoye ya shaida mata shugaba Tinubu ya yi waya da shugaban majalisar Turai, Charles Michel, ya kuma nemi alfarma a wajensa.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Tinubu ya nemi Turai ta taimakawa Najeriya a bangarorin tsaro da magance talauci. Shi kuwa Michel ya taya sabon shugaban murnar hawa kan mulki.

Wa za su zama Hadiman Tinubu?

Kun samu labari ana hasashen Mahmud Jega, Olusegun Dada, Abdulaziz Abdulaziz da Dele Alake su zama masu yada labarai a gwamnatin Tinubu.

James Faleke, Kunle Adeleke, da Ibrahim Masari ba za su rasa kujera a mulkin nan ba. A cikin mutane uku kuma mu ke tunanin za a dauko NSA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel