Karon Farko: Majalisar Dattawa Ta Yiwa Tinubu Gata, Ta Amince Ya Yi Wasu Manyan Nade-Nade 20

Karon Farko: Majalisar Dattawa Ta Yiwa Tinubu Gata, Ta Amince Ya Yi Wasu Manyan Nade-Nade 20

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed ya tura sunayen masu ba shi shawara na musamman majalisar dattawa don amincewa da su
  • Tuni majalisar ta amince da su bayan shugaban majalisar Ahmed Lawan ya karanto bukatar Shugaba Tinubu ba tare da ba ta lokaci ba
  • Ahmed ya sanarwa majalisar cewa takardar ba ta dauke da sunayen wadanda za a bai wa mukamin, amma ana bukatar amincewarsu

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.

Sanarwar wanda shugaban majalisar, Ahmed Lawan ya karanta a yau Talata 6 ga watan Yuni, ta samu amincewar majalisar.

Majalisar dattawa
Majalisar Dattawa Ta Yiwa Tinubu Gata, Ta Amince Ya Yi Wasu Manyan Nade-Nade 20. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Sai dai Shugaba Tinubu bai bayyana sunayen wadanda za a bai wa mukamin masu ba da shawarar ba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Wa Lawan Da Gbajabiamila Sabon 'Aiki' Mai Muhimmanci

Majalisar ba ta ba ta lokaci ba wurin amincewa ta bukatar

Gidan talabijin na Channels ya tattaro cewa bayan karanta takardar daga bakin shugaban majalisar, Ahmed Ibrahim Lawan, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar cikin gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban majalisar ya ce yana ‘bukatar amincewa cikin gaggawa’ saboda shugaban ya samu wadanda za su taya shi aiki don kawo ci gaba ga Najeriya.

A cewarsa:

“Saboda babu sunan daya daga cikin masu ba da shawaran, kawai mu amince daga nan.
“Muna tsammani wannan bukatar gaggawa ce daga shugaban kasa.

Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan nadin Femi Gbajabiamila mukami

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatansa.

Yayin da ya nada tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Har ila yau, an nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata na Gwamnatin Tarayya.

An rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa na 16 tun bayan samun yancin kan kasar Najeriya a shekarar 1960.

Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari Matsayin SGF

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ya kuma nada Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel