Aisha Buhari Ta Magantu, Ta Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta

Aisha Buhari Ta Magantu, Ta Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta

  • Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta ce shirin mijinta na inganta bangaren ilimi a Najeriya ya samu tagomashi daga NAFOWA
  • NAFOWA, wata ƙungiya mai zaman kanta, ta zuba hannun jari a tsarin ilimin Najeriya ta hanyar gina makarantu a sansanin sojin sama a faɗin ƙasar nan
  • Aisha Buhari ta ce gina makarantu yana taimaka wa matasa wurin samun mahallin karatu mai kyau da za'a yi gogayya da su a duniya

Abuja - Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta jaddada kudirin mai gidanta, shugaba Buhari, na tabbatar da kowane ɗan talaka a Najeriya ya samu ilimi.

Ta faɗi waɗan nan kalamai ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023 a wurin bikin kaddamar da makarantar sakamdiren ƙungiyar matan sojojin saman Najeriya (NAFOWA), Asokoro, Abuja.

Nafowa.
Aisha Buhari Ta Magantu, Ta Jaddada Kudirin Mijinta Na Samar da Ilimi Mai Nagarta Hoto: NAF
Asali: Facebook

A taron wanda wakilin Legit.ng Hausa ya halarta, Aisha Buhari ta ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Matsalar da Aka Samu Da halin da Ragowar 'Yan Najeriya Ke Ciki a Sudan

"Wannan taro babban nasara ce ga NAFOWA kuma kaddamar da wannan makarantar sakandire abun a yaba ne. Kammala aikin gina wannan makaranta yana da alfanu masu ɗimbin yawa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga cikin tagomashin aikin, ya zo daidai da kudirin mai girma shugaban ƙasa na samar da ilimi mai nagarta ga kowane ɗan Najeriya. Ina taya shugabar NAFOWA, Misis Elizabeth da tawagarta bisa wannan babban aiki."
"Na yi matukar farin ciki da gina wannan makaranta, wacce zata samarwa matasa mahallin karatu mai kyau, wanda zasu nuna bajintarsu kuma su yi gogayya a duniya."
"Bayan haka makarantar zata baiwa malamai damar koyarwa, ba da gudummuwa mai tasiri da shirya 'ya'yanmu domin zama shugabannin gobe da mabiya masu ɗa'a."

Majalisa Ta 10: Muna Jiran Jin Ra'ayin Bola Tinubu, Shugaban APC Na Ƙasa

A wani labarin kuma Shugaban APC Na Kasa Ya Fallasa Abu 1 da Suke Jira Daga Wurin Tinubu Kan Shugabancin Majalisa

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamna a Nasarawa, ya ce zasu jira su ji ta bakin shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu, kafin ɗaukar matsaya kan shugabancin majalisar tarayya ta 10.

Har kawo yanzun jam'iyyar APC mai mulki ta gaza fidda jadawalin shiyyoyin da zasu samar da shugabannin majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya ta 10 da zata fara aiki a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel