Majalisa Ta 10: Muna Jiran Jin Ra'ayin Bola Tinubu, Shugaban APC Na Ƙasa

Majalisa Ta 10: Muna Jiran Jin Ra'ayin Bola Tinubu, Shugaban APC Na Ƙasa

  • Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyya mai mulki ba ta gaggawar raba mukaman majalisa ta 10
  • Adamu, tsohon gwamnan Nasarawa ya ce suna dakon abu ɗaya daga wurin shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu
  • Ya ce ba zai yuwu APC ta yanke shiyyoyin da zasu samar da shugabannin majalisa ba dole sai da Tinubu

Abuja - Shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ba gaggawa jam'iyyar take ba wajen raba shugabancin majalisa ta 10 zuwa shiyyoyi.

Tribune ta ce Adamu ya faɗi haka ne ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023 yayin hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa (NWC) a Abuja.

Sanata Abdullahi Adamu.
Majalisa Ta 10: Muna Jiran Jin Ra'ayin Bola Tinubu, Shugaban APC Na Ƙasa Hoto: tribune
Asali: Twitter

Ya ce tsara jadawalin shiyyoyin da zasu samar da shugabannin majalisar tarayya ta 10 ba ya cikin jerin Ajendojin da suka tattauna a taron, wanda ya shafe sama da awa guda.

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Sanata Adamu ya ce jam'iyyar APC ta ƙasa ba zata ɗauki matsaya kan batun shugabancin majalisa ba tare da jin ra'ayin zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa, Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya ce:

"A'a, ba wannan batun taron yau ya maida hankali ba, duk lokacin da zamu yi taron raba muƙaman majalisa, ba zamu zauna mu kaɗai a matsayin jam'iyya ba."
"Dole idan zamu raba waɗan nan kujeru zuwa shiyya-shirya mu jawo wanda Allah ya ɗora wa nauyin jan ragamar ƙasar nan, watau zababben shugaban kasa, Bola Tinubu."
"Bayan kammala zabe ya yi tafiya zuwa waje kuma Allah ya dawo mana da shi gida a makon da ya shige, saboda haka dole da shi za'a yi kuma ba zamu hana masu buri ba, masu ganin shiyyarsu ta dace."

Kara karanta wannan

Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har yanzu babu sahihin bayani kan shiyyar da APC ta yanke kai muƙamin shugaban majalisar dattawa ko kakakin majalisar wakilai.

Tinubu Ya Baiwa Gwamna Wike Mamaki Kan Bukata 1 da Ya Nema

A wani labarin kuma Zababben Shugaban ƙasa,Bola Tinubu Ya Ba Da Mamaki, Ya Yi Watsi da Bukatar Gwamna Wike

Yayin ziyarar kwana biyu da ya fara a jihar Ribas ranar Laraba, Gwamna Wike ya roki Tinubu ya buya gwamnatin Ribas kuɗin da ta kashe wajen wasu ayyukan FG.

Da yake maida masa martani kan rokon, Tinubu ya ce Ribas ba ta biyo shi bashin komai ba amma idan suna son ya biya, Wike ya kama ƙafa da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel