Gwamna Douye Diri Ya Lashe Tikitin Neman Tazarce a Zaben Gwamnan Bayelsa

Gwamna Douye Diri Ya Lashe Tikitin Neman Tazarce a Zaben Gwamnan Bayelsa

  • Gwamnan Douye Diri, ya lashe zaben fidda gwanin da jam'iyyar PDP ta shirya ya zama ɗan takarar gwamna a zaɓe na gaba
  • Shugaban kwamitin shirya zaben fidda gwanin PDP a Bayelsa, gwamna Adeleke na jihar Osun ne ya sanar da sakamakon
  • Diri ya gode wa Deleget da kuma jam'iyyar PDP bisa damar da suka sake ba shi ya nemi tazarce karo na biyu kan madafun iko

Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya lashe tikitin zama ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar da ke tafe a karshen 2023.

Channels tv ta tattaro cewa zaɓen fidda gwani, wanda jam'iyyar PDP ta gudanar ranar Laraba 12 ga watan Afrilu, 2023, babu wani ɗan takara da ya nemi ja da gwamna mai ci.

Kara karanta wannan

A Watan Azumi, Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigan PDP 2 Sun Shiga Tsaka Mai Wuya

Gwamnan Bayelsa, Douye Diri.
Gwamna Douye Diri Ya Lashe Tikitin Neman Tazarce a Zaben Gwamnan Bayelsa Hoto: Douye Diri
Asali: UGC

Gwamna Diri ya lashe tikitin takarar da kuri'u 303 cikin jimullan kuri'u 313 da aka kaɗa a matsayin ɗan takara ɗaya tilo da babu hammaya.

Legit.ng Hausa ta gano cewa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP ya gudana ne a Cibiyar raya al'adu watau Dakta Gabriel Okara da ke Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi, shugaban kwamitin shirya zaɓen kuma gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ɗan takarar, bayan cika sharuɗɗan da doka tanada, shi ne wanda ya samu nasara.

Gwamna Diri ya yi godiya

A jawabinsa na godiya, gwamna Diri ya gode wa baki ɗaya Deleget da jam'iyyar PDP bisa sake ba shi tikitin neman tazarce kan kujerarsa a zaɓe mai zuwa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) zata gudanar da zaɓen gwamna a jihar Bayelsa ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sakataren Jam'iyyar PDP Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamna, Zai Fafata Da Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Zabaɓɓen Sanatan Bayelsa ta tsakiya, Kombowei Benson, kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, ya yaba da yanayin yadda aka gudanar da zaɓen a tsanake kuma kan doka.

PDP ta fara shirin ɗaukar mataki

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Zata Hukunta Tsoffin Ministoci da Wasu Jiga-Jigai 2 Bisa Goyon Bayan APC

Jam'iyar PDP ta aike da takardar tuhuma ga tsoffin ministoci da wasu mutum biyu, ta basu awanni 48 du kare kansu kan zargin cin amana a zaɓen gwamna a jihar Kebbi.

PDP na ta fama da rigingimun cikin gida tun kafin zaɓe har zuwa bayan babban zaɓen 2023 kuma ana ganin wannan rashin jituwa ya ja wa jam'iyar shan kashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel