Sanatan APC Ya Kawo Hujjoji, Ya Fadi Yankin da Ya Dace Sabon Shugaban Majalisa Ya Fito

Sanatan APC Ya Kawo Hujjoji, Ya Fadi Yankin da Ya Dace Sabon Shugaban Majalisa Ya Fito

  • A shekarar 2003 Osita Izunaso ya fara zama ‘dan majalisar wakilan tarayya, ya zama Sanata a 2007
  • Ganin haka ne Sanatan ya ce a duk masu harin shugabancin majalisar dattawa, shi ya fi kowa dacewa
  • Sanata Osita Izunaso yana ganin idan za ayi adalci, yankin Kudu maso gabas ya kamata a kai kujerar

Abuja - Osita Izunaso (APC-Imo) ya sake nanata cewa a halin da ake ciki a yanzu, shi ne ya fi dacewa ya karbi shugabancin majalisar dattawan kasar nan.

A ranar Talata, Vanguard ta rahoto Osita Izunaso yana mai cewa adalci, daidaito da gaskiya shi ne a bar Kudu maso gabas su fito da sabon shugaban majalisa.

Sanata Osita Izunaso yana ganin daga yankinsa ya kamata a samu wanda zai zama na uku a kasar idan aka duba cewa tun bayan 1966 Ibo bai rike mulki ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Hango Matsala a Majalisa, Sun Nemi a Dauki Matakin Gaggawa a APC

‘Dan siyasar yake cewa yana da kwarewa da sanin aikin da ake bukata wajen ganin bangaren zartarwa ya ji dadin aiki da ‘yan majalisar tarayya a Najeriya.

Osita Izunaso ya ce ya san hanya

Ganin cewa tun shekarar 2003 ya zama ‘dan majalisa, Izunaso ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewa shi ne ya dace ya zama shugaban Sanatoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga dadin aiki da za a ji tsakanin bangarorin gudanarwa da masu yin doka, Sanatan ya ce abubuwa za su lafa a yankinsa idan Ibo ya dare kujerar.

Osita Izunaso
Shugaban Kasa tare da Osita Izunaso Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Tsohon sakataren gudanarwar na jam’iyyar APC ta kasa ya ce a duk Sanatocin Kudu maso gabas, babu wanda ya sha gaban shi, ya fi kowa sanin kan majalisa.

Gogewar da Osita Izunaso ya samu

A shekarar 1992, Sanatan na Imo ya ce ya yi aiki da shugaban majalisar wakilan tarayya, Agunwa Anakwe, shi ne sakataren yada labaransa a lokacin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

Haka zalika Izunaso ya ce ya rike wannan mukami na Sakataren yada labarai a sa'ilin da Evans Nwerem ya zama shugaban majalisar dattawa a 1999.

Tun 1995 kuwa ‘dan majalisar ya yi aiki da Jim Nwobodo lokacin da ya rike Ministan matasa da wasanni. People Gazette ta fitar da rahoton nan a makon nan.

Tsakanin 1997 da 1999, ‘dan siyasar ya shaidawa ‘yan jarida cewa ya cigaba da aiki a matsayin babban sakataren yada labarai na Ministan kwadago na kasa.

An taso Obi a gaba - PCC

A zaben Shugaban kasan da aka yi a bana, an ji labari wani ‘Dan kwamitin yakin zaben shugaban kasa na jam'iyyar LP ya ce Peter Obi yana ganin barazana.

Kamar yadda yake fada, tun da Obi ya tsaya takarar shugabanci a LP, ake bin sa da kulle-kulle, har an yi kokarin a dasa mata otel saboda makiricin siyasa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Shehu Sani ya fadi sanatan da ya kamata ya gaji kujerar Ahmad Lawal

Asali: Legit.ng

Online view pixel