Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

  • Gwamnatin Birtaniya ta na lura da ‘Yan Najeriyan da suke yin kalaman da ke wuce gona da iri
  • Mataimakin Jakadan Kasar Birtaniya a Najeriya ya soki kalaman jigon APC, Femi Fani-Kayode
  • Zuwa yanzu akwai mutane da ba za su iya samun bizar shiga Ingila ba saboda sharrin bakinsu

Abuja - Birtaniya ta soki Femi Fani-Kayode wanda jagora ne yanzu a jam’iyyar APC, dalili kuwa saboda irin maganganu da ya rika yi lokacin zabe.

Mataimakin Jakadan Kasar Birtaniya a Najeriya, Ben Llewellyn-Jones ya yi hira da gidan rediyon Nigeria Info, inda aka ji ya soki Femi Fani-Kayode.

A yayin da yake kokarin tallata Asiwaju Bola Tinubu a takarar shugaban kasa, tsohon Ministan tarayyar ya caccaki wasu ‘yan takarar shugaban kasa.

Daily Trust ta iya tunawa cewa sai da ta kai hakan ya jawo jami’an tsaro na DSS suka gayyaci Fani Kayode bayan wasu maganganu da ya yi a Twitter.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa PDP Raddi Mai Ban Tsoro Bayan Dakatar da Shi Daga Jam’iyya

‘Dan siyasar ya zargi Atiku Abubakar da hada-kai da sojoji domin a hambarar da gwamnati.

A hirar da aka yi da shi, Llewellyn-Jones ya jaddada cewa kasarsa da gaske take yi wajen hana biza ga masu yin kokarin taba tsarin damukaradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya zai tafi Birtaniya Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Ana sa wa wasu ido

Rahoton The Cable ya tabbatar da zuwa yanzu akwai ‘yan siyasan Najeriya goma da suka shiga sahun mutanen a gwamnatin Birtaniya take sa wa ido.

Mu na da jerin sunayenmu, mu na duba jeringiyar mutanen amma ba mu fitar da sunaye a fili.
Na san mutane su na cewa mu rika yi (wallafa sunaye a gaban Duniya), amma mu na da dokokinmu, dokokin nan sun hana mu yin hakan.
Zuwa yanzu jerin yana kunshe da sunayen mutane tsakanin biyar zuwa goma, kuma adadin mutanen da ke cikin jerin na mu yana karuwa ne.

Kara karanta wannan

Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

Labarin nan ya yi wa Atiku Abubakar wanda ya yi takarar shugaban kasa a Jam'iyyar PDP dadi, ya yabi matakin da kasar Turan ta dauka.

Matan da za su je Majalisa

A wani rahoto, kun ji mata kusan 50 suka samu kujerun Majalisa a zaben 2023, za su goga da maza fiye da 940, kason mata bai wuce 4.7% a 2023 ba.

Mata 6 suka lashe kujerun Majalisa a Ekiti, a Kwara akwai 5, sai 4 a Akwa Ibom. Akwai biyu a Kaduna, Taraba, Kogi, Ebonyi, Ogun, Oyo da Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel