APC ta Dakatar da SGF, Jam’iyya na Binciken Sanata, An Jero Zargin da Ake Yi Masu

APC ta Dakatar da SGF, Jam’iyya na Binciken Sanata, An Jero Zargin da Ake Yi Masu

  • Shugabannin Jam’iyyar APC na Gwadabawa a Jihar Adamawa sun dakatar da Mista Boss Mustapha
  • Baya ga Sakataren gwamnatin tarayyan, za a binciki Sanata Muhammad Danjuma Goje a Gombe
  • Ana zargin Muhammad Danjuma Goje ya yi wa Gwamna Inuwa Yahaya da APC zagon kasa a 2023

Adamawa - Jam’iyyar APC ta dakatar da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a mazabarsa ta Gwadabawa da ke Jimeta a jihar Adamawa.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a ranar Laraba, ta ce jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta na zargin Boss Mustapha bai tabuka komai a Gwadabawa ba.

Duk da kujerar da yake rike da ita, wani jami’in APC a mazabar a karamar hukumar Jimeta, Muazu Kabiri ya ce Mustapha bai bada gudumuwa a zaben 2023 ba.

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

Muazu Kabiri ya koka game da yadda SGF din ya rasa rumfarsa ga jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa da kuma na Gwamnan jiha da aka yi a bayan nan.

SWC ba su yarda da haka ba

Amma shugabannin APC na matakin jihar Adamawa ba su lamunta da lamarin ba, su ka ce shugabannin mazabar ba su da ikon dakatar da shi daga jam’iyya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda rahoton ya tabbatar, Mustapha ba cikin mutane 422 da suka yi wa Bola Tinubu kamfe, PCC ya bada uzurin cewa aiki ya sa ba a tafi da shi ba.

Boss.
SGF da jami'an Gwamnati Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Muhammad Danjuma Goje

A jihar Gombe kuwa, ana tuhumar Muhammad Danjuma Goje da yi wa jam’iyyar APC zagon kasa.

Aminiya ta rahoto cewa shugabannin jam’iyyar APC na reshen Gombe sun kafa wani kwamitin mutum biyar da zai binciki Sanata Muhammad Danjuma Goje.

Kara karanta wannan

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

Kwamiti da aka kafa a garin Kashere da ke karamar hukumar Akko zai yi bincike a kan zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan na goyon bayan wata jam’iyya.

Shugaban APC na Kashere, Tanimu Abdullahi ya ce su na tunanin Goje ya hada-kai da jam’iyyar adawa a zaben Gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki da aka yi.

Tanimu Abdullahi ya ce su na da labari Sanatan ya fadawa mabiyansa su zabi wani ‘dan takara dabam, kuma ya bada kudi saboda hana APC cin zaben Gwamna.

Na kusa da Gwamnan sun yi watsi da zargin, su ka ce idan haka ne ya kamata a binciki Gwamna domin Atiku Abubakar ya karbe rumfarsa da kauyensa.

Wadanda suka yi rashi biyu

A zaben bana, an ji labarin yadda PDP da LP su ka kunyata Darektan yakin zaben Bola Tinubu, Simon Lalong da Nentawe Goshwe Yilwatda a Filato.

Sannan Yakubu Dogara ya fadi babu nauyi a zaben Shugaban kasa a PDP, ya kunyata a zaben Gwamna a APC, shi ma Aminu Tambuwal ya yi rashi biyu.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Asali: Legit.ng

Online view pixel