Sanatan Jihar Kano Ya Shiga Sahun Masu Neman Kujerar Majalisar Dattawa a 2023

Sanatan Jihar Kano Ya Shiga Sahun Masu Neman Kujerar Majalisar Dattawa a 2023

  • Barau Ibrahim Jibrin ya shiga sahun wadanda za su nemi shugabancin Majalisar Dattawa
  • Da yiwuwar Sanatan Arewacin Kano ya gwabza da Orji Uzor Kalu wajen zama na uku a kasa
  • Sanata Barau Jibrin yana ganin idan aka ajiye a batun addini, aka duba cancanta, lallai ya dace

Abuja - Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa, Barau Ibrahim Jibrin ya bayyana shirinsa na takarar shugabancin majalisa.

The Nation ta ce Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya shaidawa Duniya burinsa a lokacin da yake amsa tambayoyi daga bakin ‘yan jarida a ranar Laraba.

Sanatan na jam’iyyar APC ya fito da nufinsa karara a karon farko da yake magana da manema labarai a wajen majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja.

Barau Jibrin yake cewa nan da ‘yan kwanaki kadan, zai fara neman takarar zama na uku a kasar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Lokaci Ya Yi Da Nima Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Kalu Ya Magantu

Bayani zai fito nan da kwanaki

A lokacin, Sanata Jibrin ne Sanata na biyu da ya tabbatar da cewa yana da sha’awar rike kujerar shugaban majalisar dattawa nan da ‘yan kwanaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin shi, Sanata Orji Uzor Kalu mai wakiltar Arewacin jihar Abia ya nuna zai nemi wannan kujera, ya kuma bayyana hakan ne a ranar Talatar nan.

Majalisar Dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: @Ahmad Lawan, @TopeBrown
Asali: Facebook

Sanata Jibrin ya ce a cikin wadanda suke neman wannan kujera, shi ne mafi girma wanda ya cancanta ya jagoranci majalisa ta goma da za a kafa.

Baya ga haka, ‘dan majalisar ya yi watsi da amfani da addini da wasu Sanatoci suke yi, ya ce cancanta ya kamata a duba wajen zaben wanda ya dace.

“Ina so in fada maku cewa nayi niyyar zama shugaban majalisa ta 10 a majalisar tarayya.
Nan da ‘yan kwanaki ko mako daya ko kwana goma, zan sanar da haka a aikace, wannan shi ne buri na, ina so ina zama shugaban majalisa da yardar Ubangiji.”

Kara karanta wannan

Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

- Barau Jibril

Kira ga Bola Tinubu

Sai yanzu rahoto yake zuwa cewa Gwamnan Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya fitar da jawabin taya murna ga wadanda suka lashe zabe.

Gwamna Charles Soludo ya taya murna ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, sannan ya bada shawara cewa ya saki shugaban IPOB, Nnamadi Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel