Yanzu-Yanzu: Kotu Tayi Hukunci Kan Babban Sanatan Najeriya a Ingila

Yanzu-Yanzu: Kotu Tayi Hukunci Kan Babban Sanatan Najeriya a Ingila

  • Wata kotun Burtaniya ta samu sanata Ike Ekweremadu dumu-dumu da laifin yin safarar sassan jiki
  • Kotun ta kuma samu matar sa Beatrice da likitan su Obinna Obeta da laifi kan haɗa munaƙisar yadda za a girbi ƙodar wani matashi
  • Shari'ar ta Ekweremadu ta kwashe dogon lokaci ana yin ta tun bayan da hukumomi suka cafke shi a Ingila

Wata kotun ƙasar Ingila ta samu tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da laifin safarar sassan jiki.

Haka kuma kotun ta samu matar sa Beatrice, ƴar sa Sonia da likitan su Obinna Obeta, da laifi. Rahoton The Cable

Ekweremadu
Yanzu-Yanzu: Kotu Tayi Hukunci Kan Babban Sanatan Najeriya a Ingila Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Masu yanke hukunci sun gano cewa su ukun sun haɗa baki ne domin kawo matashin zuwa birnin Landan, su yi amfani da ƙodar sa.

Wannan hukuncin dai shine na farko irin sa wanda aka taɓa zartarwa a ƙarƙashin dokar hana bauta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam El-Rufai Ta Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Siyasa Dake Shirin Ta Da Yamutsi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafke Ekweremadu ne a shekarar da ta gabata inda aka cigada tsare shi a Burtaniya bayan hukumomi sun samu ƙorafi daga matashin game da shirin su na girbar koɗar sa.

Mai shigar da ƙara Hugh Davies KC ya gayawa kotu a ranar Alhamis cewa, iyalan Ekweremadu, da Obeta sun mayar da matashin da sauran masu son bayar da ƙoda kamar wasu kwandon shara marasa daraja. Rahoton Channels tv

"Ɗabi'ar Ekweremadu, wanda sanannen lauya kuma wanda ya gidauniyar yaƙi ɗa talauci wacce ta taimaka wajen janyo hankalin dokokin Najeriya kan hana safarar sassan jiki, ta nuna jin na isa, rashin gaskiya da munafunci." Davies ya gayawa kotu

Ya bayyana cewa Ekweremadu, wanda ya mallaki kadarori da dama kuma yake da ma'aikata sama da 80, ya amince da ya biya wani wanda yake a cikin ƙangin talauci kuɗi domin ya ba ɗiyar sa ƙoda, wanda ya nesanta kansa da shi saboda martabar siyasar sa.

Kara karanta wannan

Anyi Zazzafan Artabu Tsakanin 'Yan Bindiga Da Sojoji a Jihar Arewa, An Samu Asarar Rai

Davies ya kuma cigaba da cewa:

“Abinda ya amince yayi bai dace da rashin lafiyar ɗiyar sa Sonia ba, so yayi yayi amfani da shi, laifi ne babba. Ba hujja bace yace wai yayi hakan ne saboda son da yake yiwa ɗiyar sa."
"Neman mata magani bai kamata ya zama abinda za a yi amfani da shi ba wajen cin zalin wanda yake a cikin ƙangin talauci."

Dukkanin su, su ukun dai sun musanta tuhume-tuhumen da ake musu.

Alƙalin kotun Mr Justice Jeremy Johnson, zai yanke hukuncin sa nan gaba kaɗan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel