An Bindige Wakilin Jam'iyya Har Lahira a Wata Rumfar Zabe a Kuros Riba

An Bindige Wakilin Jam'iyya Har Lahira a Wata Rumfar Zabe a Kuros Riba

  • Ana zargin Sojoji sun harbe wakilin jam'iyya har lahira a yankin arewacin jihar Kuros Riba yayin da zabe ke gudana
  • Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta ce kamata ya yi jami'an hukumar Soji su tsaya nesa da rumfunan zaɓe
  • Wani da abun ya faru gabansa ya ce mamacin sanannen ɗan Acaba ne a Kalaba, kawo yanzu harkokin zabe sun tsaya a yankin

Cross River - Rahotanni da ke shigowa yanzu haka sun nuna cewa an harbe wakilin jam'iyya har lahira a garin Ogoja da ke yankin arewacin jihar Kuros Riba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an harbe mutumin ne a wani wuri kusa da Rumfar zaɓen da ke yankin.

Sojam Najeriya.
An Bindige Wakilin Jam'iyya Har Lahira a Wata Rumfar Zabe a Kuros Riba
Asali: UGC

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sanda reshen jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin lokacin da ta halarci wani shirin gidan Radiyo.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan ta ƙara da cewa kamata ya yi jami'an hukumar soji su tsaya nesa da wurin kaɗa kuri'a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Menene asalin abinda ya faru?

Wani ganau da abun ya faru a gabansa ya ce mamacin, wanda ake kira da suna, Joe a taƙaice, sanannen ɗan Acaɓa ne a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni dai wannan lamari ya kawo tsaiko a gudanar da zaɓe a rumfar da ke yankin.

Kawo yanzun da yawan masu kaɗa kuri'a da suka fito zabe sun tsaya cirko-cirko sakamakon kisan wakilin jam'iyyar a kusa da rumfar zaɓensu.

An tattaro cewa bisa tilas wasu 'yan jarida da INEC ta tantance su yi aikin ɗaukar fahoto a wuraren zaɓe, suka tsere a ƙasa duk da suna abun hawa.

An samu matsala a jihar Bayelsa

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin INEC, Sun Lalata Kayan Zabe a jihar Bayelsa Bayelsa

Wasu miyagun 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan daban siyasa ne sun kwace kayan zabe a Bayelsa, sun kona su kurmus.

Gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da abinda maharan suka aikata, ya roki IGP da kwamishinan yan sanda su kawo ɗauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel