Ba Za Ku Iya Kwace Wa Tinubu Nasarsa Ba, APC Ta Yi Martani Ga Obi

Ba Za Ku Iya Kwace Wa Tinubu Nasarsa Ba, APC Ta Yi Martani Ga Obi

  • Jam'iyyar APC ta zargi Peter Obi da yunkurin bin hanyoyin da su ka kaucewa doka don kwatar kujerar Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa
  • Peter Obi ya yi wani rubutu a shafinsa na Tuwita inda ya bayyana cewa ya na shiryen gudanar da zanga-zangar lumana a fadin kasar nan mai taken 'endINEC'
  • Jam'iyyar APC ta bukaci jami'an tsaro da su gargadi Obi kan tunzura jama'a, sannan ta kuma bukaci gidajen talabijin su guji bawa Obi damar yin irin kalaman

Jam'iyyar APC ta zargi dan takarar shugabancin kasa a Jam'iyyar LP, Peter Obi da yunkurin kwace kujerar Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, Daily Trust ta rahoto.

An bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu a ranar 1 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Jerin Zabbabun Sanatoci 5 Da Ke Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bayyana

Bola Tinubu
Ba Za Ku Iya Kwacewa Tinubu Nasarsa Ba, APC Ta Yi Martani Ga Obi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Peter Obi ya bayyana a ranar Litinin cewa ya na kulabalantar zaben da ya janyo aka bayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa ya na yunkurin shirya zanga-zangar 'end INEC' 'end Nigeria' a fadin kasar nan.

A wata sanarwa ranar Juma'a, dauke da sa hannun Bayo Ononuga, Daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben APC, ya ce Obi ya na ''ikirarin karya.''

Onaguga ya ce dan takarar LP ya na ''karfafa wariyar kabila da bambancin addini'' ba tare da kunya ba.

Ya bayyana kalaman Obi a matsayin ''raina kotu,'' ya ce dan takarar ya shigar da kara kotu kuma duk da haka ya ke ''kokarin haddasa abin da zai kawo tsaiko ga shari'a''.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa: IPOB Na Yi Wa Peter Obi Aiki, Jigon APC Ya Bayyana Dalilai

Ononuga ya ce jam'iyyar ta damu da ''kalaman tunzuri, haddasa fitina, da kawo rabuwar kai'' na dan takarar LP.

Ya ce:

''Dan takarar LP da ya sha kayi a zaben shugaban kasa Peter Obi har yanzu ya na zagayawa cikin kwarin gwiwa, ya na yada karya kamar lokacin yakin neman zaben shugabancin kasa, satika bayan an kammala zabe an kuma bayyana wanda ya yi nasara."

A cewar sanarwar:

''Mun damo matuka kan kalaman da ya ke yi a kafafen sadarwa na tunzurawa, karya da kuma haddasa fitina akan zaben da ya yi mummunar faduwa.
''Daga kalaman karya da Obi ya ke yi, ya na kokarin kwatar kujerar Tinubu, ta hanyar amfani da bambancin kabila da addini ba tare da kunya ba da kuma karya kiri-kiri don satar abin da ba na shi ba.
''Mu na ganin kalaman Obi a gidajen talabijin a matsayin wanda su ka saba da shari'a sakamakon ya riga ya shigar da kara kotu.''

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

Martaknin kakakin APC

Mai magana da yawun jam'iyyar ya yi kira ga jami'an tsaro da su jawa tsohon gwamnan Anambran kunne.

A cewarsa.

''Mu na kira ga jami'an tsaro da su gargade shi game da irin kalaman tunzura da ya ke yi, musumman bayan ya yi alwashin kulabalantar sakamakon zabe a kotun sauraron karrarakin zabe."
''Mu na kuma kira ga hukumar yada labarai ta kasa NBC da ta gargadi gidajen talabijin da bawa Obi damar haramta halattaccen zabe bayan ya riga ya shigar da kara kotu.''

Alakar da PDP da kulla da wasu jam'iyyu baya daga min hankali, in ji Uba Sani

A wani rahoto a baya kun ji cewa dan takarar gwamnan Kaduna a zaben 2023, Sanata Uba Sani ya ce alakar da PDP da kulla da wasu jam'iyyu ba ya daga masa hankali

Sani ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin gabanin zabe.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Lauyoyin Peter Obi sun shiga ganawa da INEC kan wani batu na zaben bana

Asali: Legit.ng

Online view pixel