Kungiyar Kiristoci Ta Darje Kujeru 2 Masu Tsoka, Ta Bukaci Tinubu Ya Ware Mata

Kungiyar Kiristoci Ta Darje Kujeru 2 Masu Tsoka, Ta Bukaci Tinubu Ya Ware Mata

  • Kiristoci sun ce kyau Bola Tinubu ya ba su kujerar Sakataren Gwamnatin tarayya idan ya shiga ofis
  • ‘Yan kungiyar Concern Christians of Nigeria su na barar kujerar Shugaban Ma’aikatan Aso Rock
  • Shugaban kungiyar John Audu-Kwaturu, ya ce ta haka ne za a iya wa kiristocin kasar nan adalci

Kaduna - Wata kungiya mai suna Concern Christians of Nigeria mai kokarin kare hakkin Kiristoci a Najeriya ta na da bukata wajen Asiwaju Bola Tinubu.

Rahoto ya zo daga Vanguard cewa ‘Yan Concern Christians of Nigeria da ke jihar Kaduna su na barar manyan mukamai a gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu.

Kungiyar ta ce tun da zababben shugaban kasar da kuma mataimakinsa watau Kashim Shettima duk musulmai ne, kyau a warewa kiristoci wasu kujeru.

Mukaman da kungiyar kiristocin ta ke nema ba kowane ba ne illa Sakataren gwamnatin tarayya da na shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

"Wannan shi ne adalci" - Kungiya

Kungiyar ta ce idan aka yi ne zai zama an yi adalci da gaskiya wajen raba kujeru a gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban wannan kungiya ta Mabiya addinin Kirista, John Audu-Kwaturu ya fitar da jawabi na musamman a ranar Alhamis, yana mika kokon bararsu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Jawabin da John Audu-Kwaturu ya fitar a garin Kaduna yana cewa kasancewar Tinubu da Kashim Shettima musulmai, hakan ya jawo abin magana.

Punch ta rahoto Shugaban kungiyar yana mai cewa shugaban kasan mai jiran gado ya yi wa kowa adalci, sannan yayi alkawarin za su rika yi masa addu’a.

"Shugaban kasa ya yi adalci ya tafi da kowa. Ba bakon labari ba ne cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da Kashim Shettima duk addinsu guda, wanda hakan ya tada kura a siyasar Najeriya.
Wannan ne karon farko tun shekarar 1999 da Mabiya addini guda za su zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shikenan: Amurka ta yarda Tinubu ne ya lashe zabe, ta yi kira mai muhimmanci ga 'yan Najeirya

Mu na cikin kiristoci da ba su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi ba, saboda haka muke kiran ayi adalci wajen raba muhimman kujeru."

- John Audu-Kwaturu

‘Yan PDP da suka koma APC da LP

Ku na da labari Bode George wanda jagora ne a jam’iyyar PDP a Kudancin Najeriya, yana tare da Peter Obi wanda ya yi takara a LP a zaben shugaban kasa.

Nyesom Wike Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Ifeanyi Ugwuanyi da Samuel Ortom sun ki bin PDP yadda Yakubu Dogara ya ki goyon bayan musulmi da musulmi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel