A Karshe Wike Ya Bayyana Wanda Ya Kori Peter Obi Daga PDP A Yayin Da Rikicin Jam'iyyar Ke Kara Ruruwa

A Karshe Wike Ya Bayyana Wanda Ya Kori Peter Obi Daga PDP A Yayin Da Rikicin Jam'iyyar Ke Kara Ruruwa

  • Gwamnan jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike ya yi zargi mai karfi game da dalilin da yasa Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour
  • A cewar Wike, Obi ya bar jam'iyyar Peoples Democratic Party ne lokacin da Sule Lamido a Jigawa cewa arewa ce za ta fitar da shugaban kasa na gaba
  • Wike ya yi wannan maganan ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin shugabannin kasa na Ohanaeze Ndi Igbo Worldwide, a Fatakwal a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris

Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribas ya yi bayani game da ainihin dalilin da yasa Peter Obi ya fita daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya koma Labour Party, LP.

Gwamna Wike ya yi magana a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris, lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin shugabannin kasa na Ohanaeze Ndi Igbo Worldwide, a gidan gwamnati a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Ƙawancen Da PDP Ta Yi Da Wasu Jam'iyyu 9 A Kaduna Baya Ɗaga Min Hankali, Uba Sani

Wike da Obi
Wike ya bayyana ainihin dalilin da yasa Obi ya fita daga PDP. Hoto: Photo credit: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa Obi ya fita daga PDP, Wike ya yi fallasa

Jigon na PDP da ke fushi da jam'iyyar ya ce kalaman Sule Lamido ne suka saka Peter Obi ya bar jam'iyyar hamayyar ya koma jam'iyyar Labour, PM News ta rahoto.

"Obi yana takara tare da mu. Na san lokacin da Obi ya tafi. Yana da halaye nagari kuma ya ce ba zai iya jure wa ba, mutane su fada gaskiya. Ya tafi Jigawa ya ga Sule Lamido, ba a Dutse ba, amma a kauye da sai ka yi tafiya na awa hudu zuwa biyar daga Dutse, babban birnin jihar.
"Kun san abin da ya fada wa Obi? Bai fada masa cewa duba ka zo a makare mun riga mun zabi wani. Ya ce arewa ce za ta fitar da shugaban kasa na gaba. Haka yasa Obi ya tafi yana cewa mai zai sa ya bata lokacinsa. Tambaye shi, haka yasa ya fita daga PDP."

Kara karanta wannan

DSS Ta Kama Mambobin Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha

Atiku ya garzaya gidan IBB a Minna sun yi ganawar sirri

A wani rahoto, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa da ke Minna.

Wazirin Adamawan ya isa filin tashi da saukan jirage na Minna da karfe 11 na safiya kuma Dr Mu'azu Babangida Aliyu, tsohon gwamnan Neja da wasu manyan mutane suka tarbe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel