Na Hannun Daman Atiku Ya Ambato Jihohin da PDP Za Ta Lashe ko Ta Doke APC

Na Hannun Daman Atiku Ya Ambato Jihohin da PDP Za Ta Lashe ko Ta Doke APC

  • Osita Chidoka yana ganin Peter Obi zai yi tasiri a zaben 2023 saboda karbuwarsa a yankin Kudu
  • Duk da haka, Chidoka bai tunanin tsohon Gwmanan jihar Anambran zai iya lashe zabe a 2023
  • Jagoran na PDP ya ce har a Kudu maso yamma akwai inda Atiku Abubakar zai ci kuri’u

Abuja - Jagora a jam’iyyar hamayya ta PDP, Osita Chidoka ya yi fashin baki da hasashen yadda yake ganin zaben shugaban kasa zai kaya.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Lahadin nan, Osita Chidoka ya amince da cewa Peter Obi zai canza fasalin siyasa.

Chidoka yana ganin ‘dan takaran na jam’iyyar LP zai kawo masu cikas, amma duk da haka ya ce bai da irin goyon bayan da zai jawo ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

PDP ta fadawa Buhari ya fatattaki shahararren Ministansa, ta fadi zunubin da ya aikata

‘Dan siyasar ya bayyana cewa PDP za ta samu kuri’u masu tsoka a wasu jihohin Kudu maso yammacin Najeriya inda Bola Tinubu na APC ya fito.

PDP za ta kai labari a Kudu maso yamma?

Oyo, Osun da Ekiti su na cikin jihohin da Chidoka yake sa ran jam’iyyar PDP ta tabuka wani abin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baya ga haka, jagoran jam’iyyar hamayyar ya hango Atiku Abubakar ya zo na biyu a jihohin Kudu maso gabas kamar Anambra, Imo da kuma Abia.

A wadannan jihohi da ke kudancin Najeriya, Vanguard ta rahoto Chidoka yana mai cewa Peter Obi na LP ne kurum zai sha gaban Atiku Abubakar.

A yankin Neja Delta da ke Kudu maso kudu kuwa, Chidoka ya na ganin akwai jihohin da jam’iyyar PDP za ta zo ta daya, a wasu kuma ta zo ta biyu ne.

Kara karanta wannan

Damammakin da manyan yan takarar shugaban kasa 4 ke da shi a jihohi 5 mafi yawan kuri'u

Atiku
Atiku Abubakar wajen kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tsohon shugaban na FRSC ya ce makomar zaben za ta kasance ne kan kuri’un Arewa, ya ce bai dace Ibo suyi watsi da PDP bayan shekaru 24 ba.

Hasashen Osita Chidoka

“PDP za a samu kuri’u babu laifi a Oyo, Osun, da Ekiti. Za mu tashi da kuri’u masu tsoka a Jihohin Anambra, Imo da kuma Abia.’
Za mu zo na biyu, Tinubu ba zai zo na biyu a Imo, Abia, Anamba da Enugu ba. APC ba za tayi nasara ba, hakan ba zai faru ba.
Za mu zo na farko ko na biyu har a Neja-Delta; a Delta, Akwa-Ibom, Bayelsa da Kuros Riba, jam’iyyar PDP za ta samu nasara.

- Osita Chidoka

Kul aka zabi Tinubu - PDP

An ji labarin yadda Mai magana da yawun kwamitin yakin zaben Atiku/Okowa ya ragargaji Bola Tinubu saboda kauracewa muhawarar ‘yan takara.

Kwamitin PDP-PCC ya ce tsohon Gwamnan Legas ba abin zabe ba ne tun da ya ki bari ayi zaman muhawara da shi, ya kuma ce ya kamata a bincike shi.

Kara karanta wannan

Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel