Jam’iyyar PDP Ta Fallasa Dabarar da Bola Tinubu Yake Son Ya Yi, Ya Dare Kan Mulki

Jam’iyyar PDP Ta Fallasa Dabarar da Bola Tinubu Yake Son Ya Yi, Ya Dare Kan Mulki

  • Kwamitin yakin takarar shugaban kasa a PDP ya soki Bola Tinubu kan rashin zuwa muhawara
  • Kakakin Kwamitin yakin neman zaben na Jam’iyyar PDP ya ce Tinubu yana neman mulki a saukake
  • Phrank Shaibu ya roki ‘Yan Najeriya su hakura da mulkin APC a 2023, su zabi Atiku Abubakar

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben kujerar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP, ya yi kira ga al’umma su gujewa Bola Ahmed Tinubu na APC.

Daily Trust ta ce kakakin kwamitin da ke taya Atiku Abubakar neman takara a 2023, Phrank Shaibu ya soki Bola Tinubu a kan kauracewa muhawara.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Lahadi, Mista Phrank Shaibu ya ce gujewa muhawarar da Tinubu yake yi, ya nuna bagas yake nema.

Shaibu yake cewa tun da aka shiga yakin neman zabe, abin da ‘dan takaran jam’iyyar APC ya yi shi ne halartar taron da abokan siyasarsa suka shirya.

Kara karanta wannan

PDP ta fadawa Buhari ya fatattaki shahararren Ministansa, ta fadi zunubin da ya aikata

An rahoto kakakin kwamitin yakin neman zaben na PDP a garin Abuja yana mai cewa Tinubu ya so a damka shi aiki ba tare da an zauna da shi ba.

Kiran da Phrank Shaibu ya yi wa mutanen Najeriya a game da zaben da za ayi a watan gobe na Fubrairu, shi ne su goyi bayan takarar Atiku Abubakar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam’iyyar APC
Yakin zaben Bola Tinubu a Jigawa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

‘Dan siyasar yake cewa Wazirin Adamawa ne ya samu karbuwa a fadin kasar nan, kuma ya nuna yada da ilmi da kwarewar da ake bukata wajen shugabanci.

Ya kamata a binciki Tinubu - PDP PCC

A jawabin da ya yi a jiya, kakakin na PDP-PCC ya yi kira ga hukumomin da ke da alhakin yaki da rashin gaskiya a Najeriya da su cafke Bola Tinubu na APC.

Vanguard ta ce Shaibu yana so a binciki ‘dan takaran na jam’iyya mai mulki domin ya yi wa Duniya bayanin hanyar da ya bi wajen mallakar dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Bukaci NDLEA Ta Kama Bola Tinubu, Ya Bayyana Dalilai

A wata hira da aka yi da shi a mujallar The News a shekarun baya, Shaibu ya ce Tinubu da bakinsa ya yi ikirarin ya dawo Najeriya bai da komai a 1998.

Mai magana da yawun kwamitin yakin zaben na PDP yake cewa a yau tsohon Gwamnan na Legas yana mai da’awar ya fi gwamnatin jihar Osun arziki.

Mutuwar Farfesa Aminu Usman

A asubar Lahadin nan aka samu labari cewa an rasa Farfesa Aminu Usman, wani kwararre a kan fannin tattalin arziki kuma Shugaba a Jami’ar Kaduna.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana alakarsa da Masanin tattalin arziki na jami’ar KASU, ya ce yana cikin masu taya shi yakin neman zaben da za ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel