PDP ta fadawa Buhari ya fatattaki shahararren Ministansa, ta fadi zunubin da ya aikata

PDP ta fadawa Buhari ya fatattaki shahararren Ministansa, ta fadi zunubin da ya aikata

  • A ra’ayin jam’iyyar PDP, Festus Keyamo SAN ya ci amanar kujerar Minista da yake rike da ita
  • Keyamo ya je kotu yana neman a tursasa hukumomi su binciki ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar
  • Kwamitin PDP-PCC yana ganin Ministan yana amfani da damarsa wajen cin ma burin APC a zabe

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP tayi kira domin a tsige Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Festus Keyamo daga mukaminsa.

Punch ta ce a ranar Lahadi 22 ga watan Junairu 2023, jam’iyyar PDP ta bukaci a tunbuke Festus Keyamo SAN a bisa zargin cewa ya ci amanar ofishinsa.

Jam’iyyar adawar tayi wannan kira ne ta bakin daya daga cikin masu magana da yawun bakin kwamitin yakin zaben Atiku/Okowa, Mista Daniel Bwala.

PDP take cewa Keyamo SAN yana amfani da kujerar da yake kai da karfin ikon Minista wajen yi wa hukumomi da ma’aikatun gwamnatin kasar barazana.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Bukaci NDLEA Ta Kama Bola Tinubu, Ya Bayyana Dalilai

Karar da Keyamo ya shigar a Kotu

Zargin da Daniel Bwala yake yi shi ne Ministan kwadagon yana amfani da kotu wajen shigar da kara a kan bangaren gwamnatin da shi yake yi wa aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya nuna PDP ta bayyana haka ne a matsayin martani bayan jin labarin cewa Lauyan ya kai kara a kotu, yana kokarin tilasta binciken Atiku Abubakar.

Festus Keyamo
Festus Keyamo a ofis Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

"Mu na kira ga Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tunbuke Ministan saboda cin amanar damar da yake da ita."

- Daniel Bwala

A cewar Kakakin kwamitin yakin takarar Atiku/Okowa a zaben 2023, Keyamo yana yin yana amfani da dukiyar gwamnati wajen cin ma burin siyasarsa.

PDP za ta cigaba da kiran taron 'yan jarida

A lokacin da Bwala ya shaidawa manema labarai wannan, akwai irin Dele Momodu a dakin taron. Jaridar Independent ta fitar da rahotonn nan kwanaki.

Kara karanta wannan

PDP Ta Jawo Danyen Rikici, Gwamna Wike Yana Barazanar Kai Jam’iyyar Zuwa Kotu

Dele Momodu wanda ya nemi tikitin takarar shugabancin Najeriya a PDP, ya ce wannan yana cikin taron manema labarai da kwamitin kamfen zai kira.

Tun farko nada karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a matsayin Mai magana da yawun kwamitin yakin zaben APC ya yi ta jawo maganganu.

A binciki Atiku - Minista

Ku na da labari Festus Keyamo yana so a binciki Alhaji Atiku Abubakar da karfi da yaji a dalilin bidiyo da aka fitar wanda ake zargin ya tona masa asiri.

Ministan tarayyar ya bada wa’adin kwanaki uku domin a fara bincike, amma ba ayi komai ba. Ganin haka Keyamo SAN ya je gaban Alkalin kotun tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel