Abin Da Zai Faru Idan Aka Ce Yau Tinubu da Kashim Ne a Mulki Inji Gwamnan APC

Abin Da Zai Faru Idan Aka Ce Yau Tinubu da Kashim Ne a Mulki Inji Gwamnan APC

  • Gwamna Bello Matawalle yace zaman Bola Tinubu zai tabbatar da tsarin karba-karba a wajen shugabanci
  • Mai girma Gwamnan ya zauna da ‘Yan S7-4-BATS-2023, ya yi alkawarin taimakawa masu tallata APC
  • Matawalle ne ke jagorantar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihohin Arewa maso yamma

Abuja - A matsayin shugaban kwamitin neman zaben shugaban kasa na APC a shiyyar Arewa maso yamma, Bello Matawalle ya tallata Bola Tinubu.

The Nation ta rahoto Bello Matawalle yana bayanin muhimmancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ci zaben da za ayi a 2023, ya dare shugabancin kasa.

Da yake wani bayani a garin Abuja, Gwamna Bello Matawalle yace nasarar Tinubu/Shettima za ta taimaka wajen ganin shugabanci yana yawo.

Gwamnan jihar Zamfara yana ganin shugabancin Tinubu zai sa a rika yin kama-kama wajen zagayawa da mulkin Najeriya tsakanin bangarorin kasar.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Fara Zuwa Gida-Gida, Sun Yi Wa Tinubu Alkawarin Kuri'u Miliyan a 2023

Jawabin Dr. Anas Anka

Kakakin Gwamnan Zamfara, Dr. Anas Anka ya fitar da jawabi a garin Abuja, yace Bello Matawalle ya yi wannan bayani da ya hadu da masoyan APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya zauna da ‘yan kungiyar S7-4-BATS-2023 da ke goyon bayan takarar Bola Tinubu da kuma Kashim Shettima a zaben shugabancin Najeriya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Ebonyi Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Mai girma Matawalle ya yi alkawarin cewa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC zai hada-kai da duk kungiyoyin da suke da ra’ayin Tinubu.

Gwamnan yace a matsayinsa na Jagoran kamfe a Arewa maso yamma, zai taimaka masu da duk abin da suke bukata wajen ganin sun samu nasara a aikinsu.

Kabiru Sani-Giant ya yi magana

Alhaji Kabiru Sani-Giant wanda shi ne shugaban wannan kungiya, yace makasudin zama da Gwamnan shi ne suyi masa bayanin irin kokarin da suke yi.

Kara karanta wannan

Mai Bakin Cin Rashawa Bai Isa ya Jagoranci Kamfen ba, Wike ga Shugaban PDP

PM News ta rahoto Kabiru Sani-Giant yana cewa suna da dinbin mabiya, wanda kwanaki suka shirya tattakin mutane fiye da 5000 a titunan jihar Kaduna.

Shi karon kansa Gwamna Bello Matawalle ya halarci wannan tattaki da aka yi kwanakin baya domin a nunawa jama’a irin gatar da Tinubu yake da shi.

LP ta samu cikas

A wani rahoto, kun ji labari ana shirin baro filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe, sai hukuma ta bada umarnin karbe jirgin saman Obidient.

An yi niyyar amfani da jirgin zuwa wajen taron yakin zabe a garin Ibadan, a karshe sai dai aka nemi wani jirgin saman dabam da ya dauki tawagar LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel