Kuri'un Wike Ba Komai Bane Ga PDP Da Atiku, In Ji Babban Jigon Jam'iyya

Kuri'un Wike Ba Komai Bane Ga PDP Da Atiku, In Ji Babban Jigon Jam'iyya

  • Daniel Bwala, kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP, ya ce ko da Wike ko babu shi Atiku Abubakar zai yi nasara a zaben 2023
  • Bwala ya ce tasirin da rashin samun goyon bayan Wike zai yi wa jam'iyyar PDP ba wani abu mai yawa bane don haka ba zai hana jam'iyyar cin zabe ba
  • Jigon na PDP ya kuma yi watsi da zargin da Wike ya yi na cewa Atiku ya ki bawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan goyon baya a 2015 yayin wani taro

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce shirin Gwamna Nyesom Wike na rashin goyon bayan dan takarar shugaban kasarta a zaben 2023 ba zai hana Atiku Abubakar samun nasara ba.

Mai magana da yawun kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP, Daniel Bwala, yayin hira a shirin Sunrise Daily na Channels Television, ya soki ikirarin da Wike ya yi na cewa Atiku ya yi wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zagon kasa.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 8, Gwamnan PDP Ya Tona Yadda Atiku Ya Wulakanta Jonathan a Zaben 2015

Gwamna Wike
Kuri'un Wike Ba Komai Bane Ga PDP Da Atiku, In Ji Babban Jigon Jam'iyya. Hoto: Gwamnatin Jihar Ribas
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A baya, Wike ya bada labarin yadda Jonathan a wata ganawa da Atiku a birnin Dorchester na Landan ya nemi goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar bayan zaben fidda gwani na PDP a 2015 amma ya ki.

A martaninsa, Bwala ya ce ikirarin da Wike labari ne kawai tunda shi (gwamnan) bai iya tabbatar da cewa yana wurin taron ba tsakanin Atiku da Jonathan a Landan.

Kalamansa:

"Abin da ya ce shi muke kira shaci-fade a shari'a. Abu ne da ya ce ya faru a Dorchester a Landan, bana wurin, babu bidiyo, kuma babu taron manema labarai. Wanda kadai zai iya tabbatar da abin da shi (Wike) ya fada shine tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ko Atiku.
"Kuma duba da cewa ba ya wurin, don haka shima bada rahoto ya ke yi kuma mafi muhimmanci, a 2015 ne; me yasa hakan ba matsala bane gare shi har zuwa lokacin da ya yi takara a zaben fidda gwani kuma sai yanzu ya ke fada?

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Sabon Bam, Ya Bayyana Yadda Atiku Ya Tozarta Jonathan a 2015

"Kana iya tambayarsa yaushe ne ziyarar karshe da ya kai wa Goodluck Jonathan. Goodluck Jonathan ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa, kuma ban ga Gwamna Wike a can ba. Yana tuntubarsa?"

PDP za ta ci zaben shugaban kasa na 2023

Da ya ke cigaba da magana, Bwala ya kara da cewa nasara na tare da jam'iyyar na hammaya a zaben shugaban kasa na 2023, rahoton Ripples Nigeria.

Ya ce ko da taimakon Wike ko babu a zaben, Atiku ne zai zama shugaban kasa na gaba kuma ya karbi mulki daga Shugaba Muhammadu Buhari.

"Jam'iyyar mu ne za ta ci wannan zaben. Rashin Wike zai iya shafar jam'iyyar kadan, misali idan ya kamata mu ci zabe da kuri'u miliyan tara ko takwas. Zai iya raguwa zuwa miliyan shida.
"Amma wannan nasarar Allah ne ya kaddara kuma zan iya fada maka, za a iya bita da kulli, hadin baki ko ma menene. Mun san sabuwar dokar zabe da abin da ta ke nufi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

"Mun ga abin da ya faru a Osun idan yan jam'iyya suka yi mata zagon kasa a jihar. Amma, me ya faru, sanata mai rawa ya yi nasara saboda mutane sun yi magana."

Wike Ya Sake Tada Kura, Ya Ce PDP Za Ta Gane 'Khaki Ba Leda Bane'

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi watsi da barazanar cewa za a kore shi daga jam'iyyarsa ta PDP.

The Nation ta rahoto cewa Wike ya bayyana cewa zai mayar da martanin da ya dace idan aka sallame shi daga jam'iyyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel