Rabiu Kwankwaso Ya Bayyana Abubuwa 2 da Zai ba Muhimmanci Idan Ya Samu Mulki

Rabiu Kwankwaso Ya Bayyana Abubuwa 2 da Zai ba Muhimmanci Idan Ya Samu Mulki

  • Rabiu Musa Kwankwaso mai neman shugabancin Najeriya a inuwar NNPP ya yi alkawarin bunkasa ilmi
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na 2023 yace gwamnatinsa za ta tallafawa matasa idan ya yi nasara a zabe
  • Sanata Kwankwaso yace babu kasar da za ta iya cigaba a Duniya sai idan ta ba harkar ilmi muhimmanci

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawari gwamnatinsa za ta bada muhimmanci kan sha’anin ilmi, idan har ya yi nasara a zaben 2023.

Daily Nigerian ta rahoto Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana wannan bayani a lokacin da ya bude ofisoshin yakin zaben jam'iyyar NNPP a Kano.

Da yake yi wa magoya bayansa da na jam’iyyar NNPP jawabi a garin Kano, ‘dan takaran yace idan ya kafa gwamnati, matasa za su koma makaranta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Zata Ba Mutane Mamaki a Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Kwankwaso

‘Dan takaran shugabancin kasar ya yi alkawari matasa za su yi farin ciki idan NNPP tayi nasara.

“Wadanda ya kamata su je makarantun firamare za su tafi, sannan kuma masu kokari za su tafi jami’o’in da ke kasashen waje.
Babu kasar da za ta iya cigaba ba tare da ta ba mutanenta ilmi mai kyau domin su bada gudumuwarsu a wajen gina kasar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso
Taron Kwankwaso da NNPP a Kano Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A lokacin da aka yi kusan watanni takwas ana yajin-aiki, Punch ta rahoto tsohon gwamnan jihar Kano yana cewa zai ware kudi domin bunkasa ilmi.

Kwankwaso wanda ya tara jama’a a wajen taron bude ofisoshin jam’iyyar ta NNPP yace hakan ya nuna mutane suna neman canjin gwamnati a Najeriya.

A jawabinsa, ‘dan siyasar ya yi kira ga magoya bayansa da mabiya jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi da su guji kalamai da za su jawo tashin hankali.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Ku goyi bayan NNPP

Dr. Aliyu Isa Aliyu wanda jagora ne a tafiyar Kwankwasiyya, yace zaben Rabiu Kwankwaso a 2023 zai sa mutanen kasar nan su samu ilmi mai nagarta.

Masanin ya yi kira ga jama’a a Facebook, su tanadi katin PVC domin su zabi Sanata Kwankwaso a babban zabe da Abba K. Yusuf (Abba Gida Gida) a Kano.

Peter Obi da Sanusi II

Kwanakin baya kun ji labari cewa Mai martaba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi bakuncin Peter Obi a gidansa da ke kasar Birtaniya.

‘Dan takaran shugabancin Najeriyan na 2023 ya je kasar Ingila domin tallata kansa. Obi yake cewa yana neman mulki ne saboda ya ceci matasan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel