Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara

Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara

  • Rikici ya sake ballewa a jam'iyyar PDP yayin da aka nemi wasu kudade Naira biliyan 10 aka rasa inda suka shiga
  • Majiyoyi sun bayyana yadda 'yan tawagar gwamnan Ribas Wike ke kokarin kawo tsaiko ga tafiyar Atiku a 2023
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da mai da hankali ga yadda za su tallata 'yan takararsu gabanin zaben 2023

Awanni 48 kafin fara gangamin kamfen na PDP, rikici ya sake barkewa a jam'iyyar kan yadda aka kashe kudin foma-foman da PDP ta siyar gabanin zabukan fidda gwani.

Kwamitin ayyukan PDP ne ke tado da wannan batu na sanin bahasin kashe Naira biliyan 10, inji rahoton The Nation.

Wasu mabobin NWC sun nuna damuwa game da yadda kudin ya zaftare daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 1.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

Rikici ya balle a PDP kan batun kudaden foma-foman takara
Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Batutuwan da ke fitowa sun ce, PDP na shirin ba dukkan mamban NWC da ke neman bahasi N28m domin rufe musu baki kan tado da sabon rikici a jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi sun ce, mambobin na NWC sun ki karbar N28m, inda suka nemi a bayyana gaskiyar inda sauran kudin suka shiga.

Tawagar Wike ce ta kitsa komai

Akwai kuma maganganun da ke cewa, wannan matsin lamba na zuwa ne daga tsagin gwamna Nyesom Wike, kuma ana tunanin tado da batun zai kai ga tsige shugaban PDP na kasa Dakta Iyorchia Ayu.

Dan takarar mataimakin shugaba kasa na PDP, kuma gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya tsorata da barazanar 'yan tawagar Wike, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki don yayyafa ma rikicin ruwa.

An ce Okowa ya damu matuka da yadda tawagar gwamna Wike ke kokarin ganin an samu baraka a tafiyar kwamitin kamfen din Atiku.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

Kudin foma-foman takarar PDP a zaben 2023

Idan baku manta ba, PDP ta siyar da foma-fomanta na takarar kujerun 2023 a farashi kamar haka:

1. Dan takarar shugaban kasa - N40m

2. Dan takarar gwamna - N21m

3. Dan takarar sanata - N3.5m

4. Dan takarar majalisar wakilai ta kasa - N2.5m

5. Dan takarar majalisun dokokin jihohi - N600,000

Bincike ya nuna mambobin NWC sun shiga mamaki da damuwar inda PDP ta kai wadannan makudan kudade da aka tara.

Barazanar da mambobin NWC ke yi

A cewar wasu majiyoyi, wasu mabobin NWC na barazanar za su daina halartar ganawar kwamitin da kuma tsame kansu daga maganar kamfen din jam'iyyar, kamar yadda The Nation ta samo.

Mambobin sun kuma bayyana cewa, dan takarar shugaban kasan PDP Atiku Abubakar ya ba jam'iyyar kudade Naira biliyan 1 gabanin zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunata ta ce:

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

"Gabanin gangamin kamfen dinmu, komai a birkice yake a jam'iyyar saboda wasu mambobin NWC sun tada jijiyar wuya game da inda N10bn suka yi na foma-foman takara.
"Suna bukatar bahasi cikin gaggawa daga jam'iyyar. Ina tunanin fushinsu ya samo asali ne daga bayanin da ya fita cewa, kudin da aka karba ya sauka da N10bn zuwa N1bn."

Jam’iyyar PDP a Zamfara Ta Fara Shirye-Shiryen Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamna

A wani labarin, jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta fara gudanar sabon zaben fidda gwanin gwamna gabanin babban zaben 2023 mai zuwa badi, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da babbar kotun tarayya ta rusa zaben fidda gwanin da aka gudanar a watannin baya, wanda ya samar da Dauda Lawan a matsayin dan takarar gwamna.

Hukuncin da mai sharia Aminu Bappa na kotun tarayya ya yanke a Gusau a makon jiya ya rusa zaben, kuma ya ba da umarnin sake zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel