'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

  • 'Dan takarar kujerar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa 'Yan Najeriya sun gaji da abinda ke faruwa a kasar nan
  • Ya sanar da cewa, dukkan miyagun abubuwa sun samu wurin zama dirshan a Najeriya kuma ba su da niyyar barin kasar
  • Yayi kira ga malamai da dattawa da su dage da addu'a tare da bai wa PDP goyon baya don ceto kasar daga halin da take ciki

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da abubuwan da ke faruwa a kasar nan, inda ya kara da cewa duk miyagun abubuwa ana samun su a kasar.

Wannan kamar yadda aka ce dawowar PDP ita ce za ta tabbatar da maido da zaman lafiya da hadewar kan yankunan Arewa da Kudu kasar nan a 2023.

Kara karanta wannan

Cin hanci: PDP ta yi martani, ta fadi dalilin da ya sa ta jika asusun bankin mambobin NWC miliyoyi

Atiku ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a yayin kaddamar da titi mai tsawon kilomita 9.5, layuka 10, 111 tare da magudanar ruwa mai tsawon kilomita 5.4 wacce aka yi a jihar Akwa Ibom.

Ya ce PDP tana da hazikan shugabanni da za su iya dawo da Nijeriya cikin martabarta a iodn duniya, ya kara da yin kira ga jama’a da su taimaka wajen dawo da jam’iyyar kan karagar mulki, jaridar Punch ta rahoto.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya wakilta a wajen taron, ya bayyana fatan goyon baya da addu’o’in dattijai da malamai wanda zai sa a iya sake kwato Najeriya kamar yadda ya bukaci kowa da kowa ya hada kai don tabbatar da tsaro.

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun gaji da abin da ke faruwa a kasar nan, duk munanan abubuwa a duniya suna nan Nijeriya, amma da goyon baya da addu’o’in dattijai da malamanmu za mu fita daga wannan matsala da muka samu kanmu a ciki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu ya ce zai ba 'yan Najeriya mamaki, zai sauya makomar Najeriya

“Muna da nagartattun shugabanni da masu ruwa da tsaki a wannan jam’iyya da za su iya kawo wa al’ummar sauyin da ake so.
"Ina taya gwamna murna kan wannan gagarumin ci gaba kuma fatan hakan zai janyo masu zuba hannayen jari zuwa jihar Akwa Ibom. Ina gode muku da kuma Allah da na kasance cikin tarihi kuma ni ne wanda zai kaddamar da wannan aiki a jihar."

Ya kara da cewa:

“Muna godiya da hangen nesa da gwamnan ya yi wajen sanya Akwa Ibom ta zama cibiyar sufurin jiragen sama, cibiyar lafiya, cibiyar samar da ababen more rayuwa hatta a harkar noma.
"Dan takarar shugaban kasa, mai hada kai ya nemi in gaya maka cewa zai tabbatar da cewa an hade kasar gaba daya daga arewa zuwa kudu domin ci gaban kasar baki daya."

A tattaunawar da Legit.ng Hausa tayi da Malama Habu Usman mazaunin Basawa a Zaria, ya bayyana cewa wannan gaskiya ne, 'yan Najeriya fa sun gaji da halin da ake ciki a kasar nan.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

"A bangaren tsaro babu labari. Kare rayuka da dukiyoyi da aka kallafawa gwamnati ma bata yi. Ga kuma matsin rayuwa da mu talaka muke ciki.
"A misali, ni na cire yarana daga makarantar kudi tunda dama kadan ta wuce ta gwamnatin saboda ba wani kudi mai yawa muke biya ba. Na mayar da su ta gwamnati. Duk abinda Allah yayi daidai ne.
"Mun gaji da matsalar da muke ciki amma fa ni bana goyon bayan kowannen 'dan takara. Muna fatan Allah ya zaba mana abinda ya fi alheri a gare mu."

- Magidancin mai 'ya'ya bakwai yace.

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya tuno yadda 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki suka yi fatali da rokon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na hakuri kan hukuncin barin jam’iyyar a 2014.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Wike ya ce gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tanbuwal yana cikin wadanda suka wulakanta Jonathan bayan taron gangamin 2014 da suka dage kan cewa wannan lokaci ne na arewa.

Ya ce kundin tsarin mulkin jam’iyyar na kunshe da tanade-tanade na shiyyoyi kan mukaman zabe da na jam’iyya inda ya koka da yadda wasu ke yin duk abin da za su iya domin yin magudia tsarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel