Rikcin Jam'iyyar PDP Na Nuna Wa 'Yan Najeriya Akwai Hadari a 2023, Wike

Rikcin Jam'iyyar PDP Na Nuna Wa 'Yan Najeriya Akwai Hadari a 2023, Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace rikicin PDP wani sako ne mara kyau ga 'yan Najeriya gabanin zuwan 2023
  • Gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa game da yaddan manyan kujeru uku na PDP ke hannun 'yan yanki ɗaya
  • Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida tun bayan ayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP ka iya shafar damar da take da shi na samun nasara a babban zaɓen 2023.

Daily Trust ta ruwaito gwamna Wike na cewa a halin yanzu PDP na faɗa wa 'yan Najeriya kar su kuskura su ba ta amana idan aka yi la'akari da yadda jam'iyyar ta gaza shawo kan rikicinta.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Rikcin Jam'iyyar PDP Na Nuna Wa 'Yan Najeriya Akwai Hadari a 2023, Wike Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai a gidan gwamnatinsa dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Yace girman kai da shugabannin jam'iyyar ke nuna wa, wanda a ganinsa ke barazana ga zaman lafiyar jam'iyyar, ba zai yi wa jam'iyyar kyau ba idan mutane suka fita kaɗa kuri'unsu a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bayanansa, gwamna Wike yace:

"Bamu lashe zaɓe ba tukunna, mun ɗauki girman kai mun ɗora wa kan mu. Muna gaya wa yan Najeriya ne, ku kula, kar ku gaskata mu, sai mu faɗi abu daban amma mu aikata wani abun na daban."

Abun da takaici komai na arewa - Wike

Gwamnan ya ƙara da cewa abun da takaici ace babu wani ɗan kudu ɗake rike da manyan kujeru uku mafi kololuwa a cikin jam'iyyar PDP.

A cewarsa, tun lokacin da PDP ta yi watsi da batun karɓa-karɓa ta fara gina matsaloli da saɓani, a cewarsa da ba'a yi watsi da batun ba da ɗan kudu zai lashe tikitin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

Bugu da ƙari, Wike yace ya zama dole a yi sadaukarwa matuƙar ana son jam'iyyar PDP ta lashe zaɓe mai zuwa.

a wani labarin kuma Atiku Ya Kara Shiga Tsaka Mai Wuya, Wasu 'Ya'yan PDP a Arewa Sun Koma Tsagin Wike

Wasu matasan jam'iyyar PDP a arewa sun koma bayan tsagin Gwamna Nyesom Wike, inda suka nemi lallai sai Ayu ya yi murabus daga kujerar shugabancin jam'iyyar.

Matasan wadanda suka gudanar da zanga-zanga a a Kaduna sun bayyana cewa PDP ba jam'iyyar arewa bace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel