Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa

Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa

  • Gwamnan Jihar Osun mai ci, Adegboyega Oyetola ya bayyana cewa ya yi imanin shine zai ci zaben gwamnan jihar da ake yi a yau
  • Oyetola ya furta hakan ne jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a mazabarsa a ranar Asabar 16 ga watan Yulin 2022
  • Gwamnan ya kuma nuna gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da zaben sumul kuma ya gamsu da yadda mutane suka fito zaben

Jihar Osun - Gboyega Oyetola, gwamnan Jihar Osun, ya ce shi mutane za su sake zaba.

Da ya ke magana da manema labarai bayan ya jefa kuri'arsa a ranar Asabar, Oyetola ya ce mutane 'suna sane' kuma sun ga bukatar su fito su yi zaben, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna PDP a jihar Osun ya bayyana dalilin da yasa yayi tsallaken layi

Oyetola Gboyega
Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce idan har ba a boye-boye a harkar, babu bukatar a rika bi ana cewa mutane su yi zabe.

"Zabe na tafiya lafiya kalau. Yana da kyau a samar da isasun na'ura domon a kammala zaben a cikin lokacin da aka kayyade," in ji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na ga jami'an tsaro. Ina ganin suna aiki mai kyau. Na ga masu zabe suna cike da izza kuma ina gode musu.
"Na yi imanin mutane sun san muhimmancin bukatar su fito su yi zabe. Idan akwai adaclci, ba sai an roki mutane su yi zabe ba. Mutane za su fito sosai, abin ya bada sha'awa.
"Da izinin Allah mai girma da buwaya, za a sake zabe na."

Oyetola ya karfafa wa magoya bayansa gwiwa

Tunda farko, a shafinsa na dandalin sada zumunta, Oyetola ya shawarci mutane kada su karaya da zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana saye da Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

Ya yi kira musamman ga magoya bayan jam'iyyar APC su fito su sauke nauyin da ke kansu na zabe cikin zaman lafiya.

Oyetola yana fafatawa ne da Ademola Adeleke na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da Yusuff Lasun, dan takarar jam'iyyar Labour Party (LP).

Dalilin da ya sa na yi tsallaken layi yayin kada kuri'a - Adeleke

A bangare guda, dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ademola Adeleke, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsallaken layi a rumfunan zaben sa domin kada kuri’arsa a ranar Asabar, rahoton PUNCH.

Da yake gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida kan dalilin da ya sa yayi tsallaken layi don kada kuri’a a gaban wadanda ya hadu da su a rumfar zabe, tsohon dan majalisar ya ce hakan ya faru ne saboda jama’a na kaunarsa.

Adeleke ya yaba da yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta shirya zaben, ya ce tsarin INEC yayi da kyau.

Kara karanta wannan

Mawaki ya ji uwar bari, ya tona cewa kudi aka biya shi domin yi wa Bola Tinubu waka

Asali: Legit.ng

Online view pixel