Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

  • Hukumar gudanar da zabe na kasa mai zaman kanta INEC ta ce ba aikin ta bane hana saye da siyar da kuri’u ba
  • Kwamitin zaman lafiya ta kasa ta bayyana damuwarta akan yadda ake siya da sayar da kur'iu a zabukan Najeriya
  • Rev. Fr. Atta Barkindo ya ce al’ummar jihar Osun suna jira su sayar da kuri’un su saboda yadda talauci ya kunno kai a kasar

Jihar Osun - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba aikinta ba ne hana sayen kuri’u a lokacin zabe.

Kwamishinan Zabe na INEC a Jihar Osun, Farfesa Abdulganiy Raji, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television na Daily Sunrise a safiyar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar cin mutuncin Buhari a Kogi

A ranar Laraba, shugaban sakatariyar, kwamitin zaman lafiya na kasa, Rev. Fr. Atta Barkindo, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake siyan kuri'u a lokacin zabukan kasar.

Malamin ya ce tuni al’ummar jihar Osun suka fara jira dan su sayar da kuri’un su a zaben da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, inda ya koka akan yadda talauci ya kunno kai a kasar.

Amma da yake magana a ranar Alhamis, Farfesa Raji ya ce:

“Game da batun sayen kuri’u, bari in gaya muku cewa INEC ba za ta iya hana sayen kuri’u ba. Za mu iya yin ƙoƙari ne kawai don ganin an hana mutane yin hakan ta hanyar wayar da kan masu jefa ƙuri'a da wayar da kan jama'a da muka yi ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

zaben
Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC
Asali: Getty Images
“Saye da sayar da kuri’u laifi ne kuma INEC ba hukumar tsaro ba ce da za ta iya kama mutane. Za mu iya sanar da jami'an tsaro ne kawai lokacin da [siyan kuri'a] ke faruwa.

Kara karanta wannan

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

Sannan a kama su (wadanda suka aikata laifin) a gurfanar da mu a gaban kuliya.

“A koyaushe ina mamakin lokacin da mutane ke magana game da sayen kuri’u da sayar da kuri’u suna sa ran INEC za ta iya dakatar da shi, lamarin da ba shi da alaka da hurumin gudanar da zabe.
"Mutanen da ke da hannu wajen siyan kuri'a da sayar da kuri'a su ne wadanda ya kamata ayi maganin su."

'Yan fashi: Matawalle ya bukaci da a tsawaita shekarun ritaya na jami'an tsaro zuwa 70

A wani labari, Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin ritayar jami’an tsaro a Najeriya zuwa shekaru 70, inda ya kara da cewa ya kamata a tsawaita shekarun shiga aikin Short Service daga shekaru 30 zuwa 32 domin samun karin ma’aikata. Rahoton jaridar PUNCH

Sai kuma a ba wa maza da mata masu karfi jiki dake son shiga aikin jami’an tsaro damar yi wa kasar su hidima don tabbatar da tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel