Mawaki ya ji uwar bari, ya tona cewa kudi aka biya shi domin yi wa Bola Tinubu waka

Mawaki ya ji uwar bari, ya tona cewa kudi aka biya shi domin yi wa Bola Tinubu waka

  • Habeeb Okikiola ya yi raddi ga masu sukarsa saboda kurum ya na goyon bayan jam’iyyar APC
  • Mawakin da ya shahara da suna ‘Portable’ ya bayyana cewa kudi aka biya shi domin ya yi waka
  • Portable ya ce akwai lokacin da aka biya shi domin ya caccaki Tinubu, kuma ya yi abin da ya saba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Matashin mawakin nan mai tasowa, Habeeb Okikiola, ya yi bayanin abin da ya sa aka ji yana yi wa jagororin jam’iyyar APC mai mulki waka.

Habeeb Okikiola wanda aka fi sani da Portable a Duniyar wake-wake, ya fitar da wani bidiyo a shafinsa na Instagram, yana maidawa masu suka amsa.

Ganin cewa yana goyon bayan jam’iyyar APC ne a zaben gwamnan Osun, mutane a dandalin sada zumunta sun tasa mawakin a gaba, su na sukarsa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya fadi abu 1 da zai bar wa ‘Ya ‘yansa gado idan ya bar Duniya

Da yake bayani a wannan bidiyo da ya wallafa a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli 2022, Portable ya ce kudi aka biya shi, don haka aikinsa kurum yake yi.

The Cable ta fassara bayanin mawakin, inda aka rahoto shi yana nuna ba a wasa da sana’a.

Na taba zagin Tinubu a waka -Portable

An ji Portable yana cewa akwai lokacin da wasu suka biya kudi domin ya zagi Bola Tinubu a wakarsa, kuma hakan aka yi, a karshe aka biya shi kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Portable
Habeeb Okikiola watau Portable da Bola Tinubu Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Wannan karo kuma reshe ya juye da mujiya, mutanen Tinubu ne suka biya kudi domin a tallata ‘dan takaran shugaban kasa da na gwamnan Osun.

“Idan aka biya ka kudi, dole ka yi aiki. An taba biya na kudi domin in caacaki Tinubu a lokacin zanga-zangan da aka yi.”

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

“Amma tun tuni aka yi wannan. Yanzu jam’iyyar APC ta ce Akoi Tinubu.”
“Muddin sun biya ka, sai ka yi aikinka, babu wasa. A lokacin da aka bukaci in zagi Tinubu, na karbi kudi, na yi aiki na.”
“Yanzu Tinubu ne na gaba. Su suka ba ni kudi, don haka dole ya zama dole in yi aikin kudin da na karba. Akoi APC.”

Rigimar APC a Ribas

A baya an samu rahoto Magnus Abe ya ce ‘Dan takaran Gwamnan jiharRibas bai cikin ‘ya ‘yan jam’iyya, kuma bai bada gudumuwar komai a APC ba.

Saboda wannan ne da kuma wasu dalilai na zargin satar kudi, tsohon Sanatan yace ba zai bata lokacinsa wajen yi wa APC kamfe a zaben gwamna ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel