Dalilin da ya sa na yi tsallaken layi yayin kada kuri'a - Adeleke

Dalilin da ya sa na yi tsallaken layi yayin kada kuri'a - Adeleke

  • Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ademola Adeleke ya bayyana dalilin da yasa tsallaken layi yayin kada kuri'a
  • Isiaka Adeleke ya yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC akan tsarin shirya zabe
  • Adeleke ya ce yana son zaben jihar Osun ya zama abun koyi yayin da kasar ke tunkarar zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Osun - Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ademola Adeleke, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsallaken layi a rumfunan zaben sa domin kada kuri’arsa a ranar Asabar. Rahoton PUNCH

Da yake gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida kan dalilin da ya sa yayi tsallaken layi don kada kuri’a a gaban wadanda ya hadu da su a rumfar zabe, tsohon dan majalisar ya ce hakan ya faru ne saboda jama’a na kaunarsa.

Kara karanta wannan

Saura kwana 2 zaben Osun, Jam’iyya ta sa ‘Dan takarar Gwamna ya janye takara

“Mutane ne suka gayyace ni da in zo na kada kuri’a ta in wuce”.
OSUNI
Dalilin da ya sa na yi tsallaken layi yayin kada kuri'a - Adeleke FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Adeleke ya yaba da yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta shirya zaben, ya ce tsarin INEC yayi da kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dangane da rade-radin sayen kuri’u da ‘yan adawar siyasa ke yi, ya ce yanzu fara zabe kuma fatan shi rahoton ya tsaya a rade-rade.

“Muna son wannan zabe ya zama abun koyi a shekarar 2023. Duk duniya na kallonmu kuma wannan zai zama jarabawa garemu baki daya. Don haka mutanen Osun su zabi wanda suke so,” inji shi.

Yadda Tinubu ya guji gwamnonin Arewa-maso-Yamma, ya dauki Shettima

A wani labari, Cikakken bayani akan yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya kaurace wa zaben gwamnonin Arewa maso Yamma, a matsayin abokin takararsa ya fito. Rahoton PUNCH

Maimakon ya yi kasa a gwiwa akan matsin lamba da gwamnonin suka yi masa, a ranar Lahadin da ta gabata Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel