2023: Ana rikici kan mataimakin Tinubu, Ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar APC

2023: Ana rikici kan mataimakin Tinubu, Ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar APC

  • A dai-dai lokacin da jam'iyyun siyasa ke kokarin cika ka'idar INEC na miƙa yan takara, jam'iyyar APC ta yi babban rashin ɗan majalisar
  • Mamba mai wakiltar wata mazaɓa daga jihar Oyo a majalisar wakilai ta ƙasa, Shena Peller, ya sanar da ficewa daga APC
  • Ya ce mako mai zuwa zai sanar da sabuwar jam'iyyar da zai koma, ana ganin ya yi haka ne bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Oyo- Mamba mai wakiltar mazaɓar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa, jihar Oyo a majalisar wakilan tarayya, Shina Peller, ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress APC.

Daily Trust ta ruwaito cewa ɗan majalisar ya sanar da haka ne a wani rubutu da ya saki ranar Jumu'a yana mai cewa, "Salon tafiyar da jam'iyyar a jihar Oyo ya kashe masa kwarin guiwa."

Kara karanta wannan

Abu ɗaya zai ceci APC ba zata sha kaye a zaɓen 2023 ba, Abdullahi Adamu ya magantu

Shina Peller.
APC ta yi babba rashi ana shirin 2023, Ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Honorabul Peller ya ƙara da cewa haƙurin cigaba da zama a APC wanda ya yi a baya ya illata masoyan sa, musamman matasa masu tasowa.

A kalamansa, Ɗan majalisar wakilan tarayyan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na yi iya bakin kokari na a APC, yanayin salon tafiyar da demokaraɗiyyar cikin gida a reshen jam'iyya na jihar Oyo ya kashe mun duk wani kwarin guiwa da burina kuma ya zama wajibi na duba abin da magoya bayana ke so."
"Na fahimci cewa matasa da sauran mutane zasu cigaba da bauta wa wasu kalilan da tauraruwar su ta ɗaga sama."

Wace jam'iyya ya koma?

Mista Peller ya sanar da cewa nan ba da jimawa zai bayyana wa duniya sabuwar jam'iyyar da ya koma, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

"Zan sanar da sabuwar jam'iyyar da zan koma a ranar Talata 22 ga watan Yuni, 2022."

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Okowa ya cancanci zama mataimakin Atiku, PDP ta fitar da sakamakon tantancewa

Honorabul Peller wanda ya samu nasarar ɗarewa kan kujerar majalisa karkashin inuwar APC a zaɓen 2019, ya nemi tikitin takarar sanatan Oyo ta arewa don fafatawa a zaben 2022 amma ya sha ƙasa.

A wani labarin kuma shugabannin kudu da arewa ta tsakiya sun jefa mataimakin Atiku cikin tsaka mai wuya, sun aike masa da zazzafan sako

Shugabannin kudancin Najeriya sun yi watsi da matsayin mataimakin da aka ba gwamna Okowa na jihar Delta.

A wata sanar da shugaban kungiyoyin suka fitar, sun bayyana cewa Okowa wanda aka cimma matsayi a jiharsa ya ci amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel