Shirin 2023: Shugaban PDP ya bayyana lokacin da za a sanar da abokin tafiyar Atiku

Shirin 2023: Shugaban PDP ya bayyana lokacin da za a sanar da abokin tafiyar Atiku

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, tuni ta kammala shiri domin bayyana sunan wanda zai yi takara da Atiku
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Atiku Abubakar ya gama yanke wanda zai zaba kamar yadda shugaban PDP ya bayyana
  • A yau dai saura akalla sa'o'i 48 ga jam'iyyun siyasan Najeriya su bayyana cikakkun 'yan takararsu na shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin sa’o’i 48 masu zuwa, za su fadi abokin gamin Atiku gabanin zaben 2023.

Ayu ya ba da wannan tabbacin ne a jawabin bude taron da ya yi da mambobin kwamitin tuntuba da aka kafa domin taimakawa Atiku wajen zaben wanda zai yi takara tare dashi.

Kara karanta wannan

Abokin tafiyar Atiku: PDP ta rage, tana duba hada Atiku da daya cikin wasu jiga-jigai 3

An zabi abokin gamin Atiku a PDP
Shirin 2023: Za mu sanar da waye abokin tafiyar Atiku nan da sa'o'i 48, inji shugaban PDP | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ayu na ganawar sirri da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Ya bayyana cewa taron na ci gaba da tuntubar juna da nufin kaiwa ga zabin da ‘yan Najeriya za su yi murna da samu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ayu ya ce:

“Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu zai zo nan, amma da safiyar nan sai ya yi karo da wani uzurin.
“Ya ba da hakuri kuma idan ya zo da wuri, zai zo nan wurin mu. Amma za mu ci gaba da aikin da ya ba mu.
“Dan takarar ya rubuta mana a matsayin mu na bangaren gudanarwa na jam’iyyar kan zabin abokin takararsa."

Taron da ke gudana ya samu halartar Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal; Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, inji Vanguard.

Kara karanta wannan

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Hakazalika da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark; tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko; Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da Sanata Philip Aduda da dai sauran su.

An ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, ta baiwa jam’iyyun siyasa har zuwa ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, 2022, su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da abokan takararsu.

Ka zabi daya: Shehu Sani ya tada kura a intanet, ya nemi Osinbajo ya zabi Atiki ko Tinubu

A wani labarin, sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, Shehu Sani, ya ce ya tambayi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabi dan takarar shugaban kasa kafin zuwan 2023.

Sani a wani sako da Legit.ng ta gani a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, ya ce ya roki Obasanjo ta Whatsapp da ya zabi dan takara tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Babu daga kafa: Duk da Atiku ya taya shi murna, Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

Tsohon sanatan ya kara da cewa zai yi wa mabiyansa bayani a dandalin sada zumunta idan tsohon shugaban kasar ya amsa masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel