Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

  • Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi ta dakatar da wata ma'aikaciya saboda shiga harkar siyasa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar APC, wanda aka ce ta shiga
  • Rahoton da muka samu ya ce, an ga ma'aikaciyar na tallata wasu 'yan takarar kujerun siyasa na jam'iyyar APC

Bauchi - Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tatari Ali a Bauchi, ta dakatar da wata babbar ma’aikaciya, Misis Raliya Kashim, bisa zargin hannu dumu-dumu a shiga siyasar da ya sabawa dokar aikin gwamnati.

Kakakin kwalejin, Malam Maimako Baraya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Bauchi, Punch ta ruwaito.

Baraya ya ce an dakatar da Raliya ne saboda yi wa wasu ‘yan takarar shugaban kasa da na gwamna kamfen ta shafinta na WhatsApp.

Kara karanta wannan

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

An kori wata ma'aikaciyar Poly saboda shiga siyasa
Aikin gwamnati: Lakcaran Poly a Bauchi ta rasa aikinsa saboda shiga siyasa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sanarwar ta bayyana sakin layin doka ta 1.4.1.9 ta aikin gwamnati da ta haramta irin wannan dabi'a, Tribune Online ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Kwanan nan ma’aikaciyar ta yada faifan bidiyo dauke da kayan yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC wanda hakan ya saba wa ka’idar da’a ta ma’aikatan gwamnati.
“Mahukuntan kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali suna son bayyanawa balo-balo cewa cibiyar kwararru ce da ke tafiya da ka’idoji kuma ba za ta bar wata kafa ba wajen tabbatar da cewa duk ma’aikata sun mutunta dokokin cibiyar.
"Muna so mu tabbatar wa jama'a cewa babu wani shafaffe da mai kuma ba gudu ba ja da baya a kalubalantar ayyukan ma'aikatan siyasa da makiya jihar."

Raliya Kashim ta kasance mataimakiyar Janar Manaja na ayyukan kwararru na Kwalejin kafin dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Babbar magana: Majisar dokokin jihar Arewa ta tsige kakakinta, da wasu 3 saboda dalilai

A wani labarin, an tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi Rt Hon Ahmed Muhammed da wasu manyan jami'an majalisar dokokin jihar guda uku.

Majalisar ta dauki wannan mataki mai tsauri na ladabtarwa ne yayin wani taron gaggawa da aka yi a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, inji rahoton Punch.

Manyan 'yan majalisar uku da aka kora daga majalisar sun hada da shugaban masu rinjaye, Bello Hassan Balogun, mataimakin shugaban masu rinjaye, Idris Ndako, da kuma Hon Edoko Moses Ododo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel