Akwai ƙura: Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba

Akwai ƙura: Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba

  • Masu ruwa da tsaki daga bangaren Kudu maso gabashin kasar nan su na neman tada zaune tsaye a PDP
  • Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka fito daga kasar Ibo su na adawa ga takarar Gwamna Nyesom Wike
  • Dalilinsu yankin ya yi mulki daga 2010-2015, kuma Wike ya taba cewa bai sha’awar yin mataimaki

Abuja - Biyo bayan shawarar da ‘yan kwamitin kasa da majalisar NWC na jam’iyyar PDP suka bada, wasu sun fara nuna adawa ga Nyesom Wike.

Rahoton Daily Trust na yammacin yau ya ce wasu jagororin jam’iyyar PDP daga yankin Kudu maso gabas sun nuna ba su gamsu da Gwamna Wike ba.

Wadannan masu ruwa da tsaki sun nuna babu adalci idan har Atiku Abubakar ya zabi Wike.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Masu adawa ga gwamnan jihar Ribas su na ganin ba zai yiwu bayan kudu maso kudu sun amfana da Goodluck Jonathan ba, a sake ba su takara ba.

Dr. Goodluck Jonathan wanda ya fito daga Neja Delta ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa, daga baya ya zama shugaban Najeriya na shekara biyar.

Rahoton ya ce ana zargin masu wadannan ra’ayi ne suke fito da wasu tsofaffin bidiyoyi a kafafen sada zumunta wadanda za su sa Wike ya lashe amansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Nyesom Wike
Nyesom Wike yana kamfe a Abia Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

A bidiyon an ji Gwamnan a lokacin yana neman tikitin jam’iyyar PDP yana rantsewa cewa ba zai karbi tayin takarar mataimakin shugaban kasa a 2023 ba.

Tun da har tsohon ‘dan takarar ya fadawa Duniya bai sha’awar kujerar, suka ce sai a hana shi.

A cewar masu wannan ra’ayi, idan aka ba mutumin kudu maso gabas takara ne za a samu zaman lafiya a jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

Majiyar ta shaidawa jaridar cewa kowane ‘dan takara yana harin yin wasoso a bangaren Kudu maso kudu, don haka zai fi kyau Atiku ya dauki Ibo a PDP.

Vanguard ta ce tsohon Gwamnan Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani yana da wannan ra'ayi, ya koka da cewa tun 1999, an ki bari Ibo su dandana mulki.

Mabanbantan rahotanni sun tabbatar da Nyesom Wike ya yi wa sauran wadanda ake tunani kafa a wajen zama ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya.

Kun ji yadda ‘yan kungiyar IMG ta mutanen Neja Delta da ke zama a Turai da Amurka su ka nuna goyon-bayansu ga Gwamna Nyesom Wike a tikitin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel