Tinubu zai shiga farautar Mataimakinsa gadan-gadan, watakila a tsaida Gwamna mai-ci

Tinubu zai shiga farautar Mataimakinsa gadan-gadan, watakila a tsaida Gwamna mai-ci

  • Asiwaju Bola Tinubu zai yi zama da Gwamnoni nan ba da dadewa ba domin tsaida abokin takara
  • ‘Dan takarar shugaban kasa na APC mai mulki yana neman wanda zai zama mataimakinsa a 2023
  • Babu mamaki PGF ta taka rawar gani wajen dauko wani daga Arewa maso yamma ko maso gabas

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da abokin karawarsa na PDP, Atiku Abubakar sun shiga neman mataimaka.

Da Punch ta yi hira da Bayo Onanuga wanda shi ne mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zabe, ya ce Bola Tinubu zai hadu da gwamnoni.

Bayan wannan zama ne ake sa rai ‘dan takarar zai zakulo wanda za su shiga zabe tare a 2023. Sai dai har zuwa yanzu ba a sa lokacin da za ayi taron ba.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Onanuga ya fadawa ‘yan jarida cewa Tinubu ya yi alkawari da gwamnonin APC cewa muddin ya zama ‘dan takara, a cikinsu ne zai dauko mataimakinsa.

A cewar tsohon ‘dan jaridar, Bola Tinubu ya fi son ya tafi da sauran kusoshin jam’iyya, a maimakon ya dauki mataki shi kadai ba tare da tuntuba ba.

Daga ina zai fito?

Mai magana da yawun bakin masu yakin neman zaben ‘dan takarar ya ce Ubangidan na su yana da damar da zai dauki abokin takara daga duk inda ya so.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: UGC

An rahoto Alhassan Ado Doguwa yana mai cewa a yarjejeniyar da aka yi a APC, daga Arewa maso yamma ne ya kamata mataimakin shugaban kasa ya fito.

Akwai kuma masu ganin ya kamata a dauko wani babba ne a APC daga Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban kasa ya nemi ya jawo kwamacala a APC wajen fito da ‘Dan takaran 2023

“Jagororin jam’iyya za su duba yiwuwar cin zabe, su ga yadda za ayi wa kowa adalci. Watakila a dauko daga Arewa ta yamma ko gabas ko tsakiya.”
“Haka ake yi. Ba za a zagaye jam’iyya ba. Kungiyar gwamnonin APC a karkashin Atiku Bagudu ke da nauyin nema masa wanda zai zama mataimaki.”

- Bayo Onanuga

Babu baraka a APC

A cewar Onanuga, Tinubu yana da kyakkyawar alaka da kusan duka gwamnonin jihohin APC don haka ba za a samu matsala a kan wanda za a tafi da shi ba.

Rahoton ya ce zuwa karshen makon nan ake sa ran Bola Tinubu zai zauna da jagororin jam’iyya; daga ciki har da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Atiku ya na lissafi

Yayin da Tinubu yake neman wanda zai zama abokin takararsa a tikitin APC, an samu rahoto shi kuma Atiku Abubakar ya shiga taro da gwamnonin hamayya.

Kara karanta wannan

Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba

Kamar yadda Atiku bai dauki abokin takararsa ba, Onanuga ya ce su ma ba kai ga yin zabi ba, amma a na su bangaren, ‘ya ‘yan jam’iyya su na da ta-cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel