Ayo Fayose ya rubutawa Tinubu wasika, ya ankarar da shi barazanar da yake ciki saboda takara

Ayo Fayose ya rubutawa Tinubu wasika, ya ankarar da shi barazanar da yake ciki saboda takara

  • Ayodele Peter Fayose ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Bola Tinubu mai neman takara a APC
  • Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya nunawa 'dan takarar cewa rayuwarsa ta na fusakantar barazana
  • Duk da ba ya PDP, Fayose a matsayinsa na Bayarabe ya bukaci jigon na APC ya yi hattara da takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya rubuta budaddiyar wasika ga Asiwaju Bola Tinubu a kan maganganun da ya yi a Ogun.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan wasika da jigon na jam’iyyar PDP ya aikawa Bola Tinubu.

A wasikar da Ayo Fayose ya fitar a shafin Twitter a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni 2022, ya ce ya yi la’akari da zamansa Bayarabe ne ba wai ‘dan siyasa ba.

Kara karanta wannan

Abinda aka yiwa Awolowo da Abiola ake kokarin yiwa Tinubu, Ayo Fayose

“Ina so in bayyana cewa ni ba ‘dan jam’iyyar APC ba ne, kuma ba zan taba zama ba.”
“Ina rubutu ne la’akari da abubuwan da na lura da su da kuma yiwuwar shiga hadarin da kai karon kanka ka ke ciki nan gaba.”
“Na kuma karanta martanin abokan hamayyarka a Kudu da Arewa. Martanin na su ya tada mani hankali game da rayuwarka.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina hango barazana!” - Ayo Fayose.
Ayo Fayose ya rubutawa Tinubu wasika
Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Yadda aka yi wa Abiola da Awolowo

The Cable ta ce Ayo Fayose ya gargadi Tinubu a kan yadda aka yaudari Obafemi Awolowo da Moshood Kashimawo Abiola, a karshe aka kai su, aka barosu.

A matsayinsa na wanda ya san tarihi, Fayose ya ankarar da Bola Tinubu kan yadda na-kusa da shi za su iya zuga shi ya yi fatali da shawarar da yake ba shi.

Kara karanta wannan

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Lura da abin da ya gani, wasikar ta fadawa mai neman takarar a APC cewa an raba kan magoya bayansa, kuma za ayi masa irin na MKO Abiola da Awolowa.

Wasikar tsohon gwamnan na Ekiti ta kare da wasu ayoyi daga Injila da suka ce masu hankali su na hango masifa, amma wasu za suyi yunkurin auka masa.

Matsayar Gwamnoni

A ranar Litinin aka ji labari Gwamnonin Arewacin Najeriya su na nan a kan matsayarsu na cewa sai an ba kudu takara a 2023, duk ba su tare da Ahmad Lawan.

Gwamna Simon Bako Lalong ya fadawa Duniya cewa abokan aikinsa sun yi zama da Muhammadu Buhari a Aso Villa, sun nanata masa matsayinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel