Zaben Ahmad Lawan zai barka Gwamnonin APC, sun ce dole mulki ya koma Kudu a 2023

Zaben Ahmad Lawan zai barka Gwamnonin APC, sun ce dole mulki ya koma Kudu a 2023

  • Gwamnonin Arewacin Najeriya su na nan a kan matsayarsu na cewa sai an ba kudu takara a 2023
  • Gwamna Simon Bako Lalong ya ce abokan aikinsa sun yi zama da Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Matsayar Gwamonin shi ne a ba ‘Dan kudu takara, ba su goyon bayan APC ta tsaida Ahmad Lawan

Abuja - Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya da ke mulki a karkashin jam’iyyar APC sun dage a kan bakarsu na cewa dole shugabancin ya bar Arewa

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa gwamnonin sun yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayanin cewa matsayarsu shi ne a maida shugabanci zuwa Kudu.

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Bako Lalong ya yi wa manema labarai jawabi bayan sun gana da Mai girma shugaban kasa dazu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan dan takarar da yake so ya gaje shi

Bayan taron da aka yi a fadar Aso Villa a Abuja, Gwamna ya ce abokan aikinsa 13 sun ba shugaban kasa hakuri saboda yadda aka fitar da matsayar.

Takardar da gwamnonin suka sa hannu ya shiga hannun ‘yan jarida kafin shugaban kasa ya ji.

Simon Bako Lalong ya ke cewa sun yanke wannan hukunci ne saboda adalci da zaman lafiya ganin cewa Muhammadu Buhari zai yi shekaru takwas a ofis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnonin APC
Tinubu da Gwamnonin APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Gwamnan na Filato ya kuma bayyana cewa duka gwamnonin APC na Arewa za su sake haduwa da juna a kan maganar wanda za a ba takara a zaben 2023.

Shugaban kungiyar gwamnonin ya ce Mai girma Muhammadu Buhari ya saurari maganar da su ka yi masa na cewa a fitar da ‘dan takara ta hanyar adalci.

Har ila yau, Gwamnan ya bayyana cewa Buhari ya bada umarni su hadu da shugabannin jam’iyyar APC na kasa kan maganar wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Yahaya Bello ya yi burus

Gwamna Yahaya Bello bai halarci wannan zama ba domin ya ce babu sa hannunsa a matsayar.

Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce babu laifi don Yahaya Bello ya ki zuwa wajen wannan taro domin kuwa da tsarin farar hula ake amfani.

Lawan ne 'Dan takara - Adamu

An ji labari cewa rikici ya barke a jam’iyyar APC biyo bayan sanarwar da shugaban jam'iyya, Abdullahi Adamu ya bada na wanda ake so ya yi takara a 2023.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan shi ne zabin jam'iyya a matsayin 'dan takarar shugaban kasa kamar yadda Sanata Abdullahi Adamu ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel