Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

  • Rikici ya kunno kai a APC yayin da shugaban APC ya ce, kwamiti ya zabi maslaha, ya zabi Ahmad Lawan ya gaji Buhari
  • Rahotanni sun bayyana cewa, za a ba sauran 'yan takara damar gwabzawa a zaben fidda gwanin APC da ake yi
  • Sai dai gwamnonin APC na Arewa sun yi bore, inda suka dage dole a mika mulki yankin Kudancin kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rikici ya barke a jam’iyyar APC biyo bayan sanarwar da shugaban APC Adamu ya sanar da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa da kwamiti ya amince dashi, Sanata Abdullahi Adamu ya yi.

Adamu ya bayyana hakan ne a taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC ranar Litinin a Abuja rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya magantu kan dan takarar da yake so ya gaje shi

Da dumi-dumi: Adamu ya bayyana Lawan a matsayin dan takarar maslaha daga Buhari
Da dumi-dumi: Adamu ya bayyana Lawan a matsayin dan takarar maslaha | Hoto: Channels Tv
Asali: Facebook

Sauran ‘yan takarar da suka hada da Asiwaju Bola Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Dokta Kayode Fayemi da David Umahi, da dai sauransu za a ba su damar gwabza zaben fidda gwani a taron da za a yi gobe a dandalin Eagle Square, Abuja.

Membobin NWC sun dage cewa dole ne a ba wa sauran masu 'yan takara matakin da za su fafata a zaben, kamar yadda The Nation ta ruwaito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amincewar Adamu na Lawan a matsayin yardajjen dan takara ya saba wa matsayin gwamnonin APC 11 na Arewa, wadanda suka amince da cewa mulki ya kamata ya koma Kudu bayan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Adamu ya shaidawa kwamitin ayyuka na kasa na APC cewa Lawan ne bayan ya tattauna da shugaba Buhari.

Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa

Kara karanta wannan

Zaben Ahmad Lawan zai barka Gwamnonin APC, sun ce dole mulki ya koma Kudu a 2023

A wani labarin, kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa a APC a ranar Juma’a ya musanta batun tantance tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin 'yan takara.

Shugaban kwamitin tantancewar, John Odigie-Oyegun, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abduallahi Adamu, a wani taron kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa.

Odigie-Oyegun ya shaidawa manema labarai cewa sabanin labaran da ake yadawa, tsohon shugaban bai halarci taron tantancewan da aka yi Transcorp Hilton ba, inji rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel